Kannywood

M U T U M B A Y A B A D A D A U K A K A Karanta Abinda Shima Babban Darakta Falalu Dorayi Akan Bashar Chiroki

Allah shi yake kaddarawa bawa  samu da rashi, wanda Allah ya nufe shi da zama cikin kunci ko rashin wadatar abubuwa da saba rayuwa dasu, ba kaskanci ba ne face jarraba da kuma kaddarar Allah akansa.

Mai hankali yasan duniya bala’ice gida ne na jarrabawa tsakanin wadata da tsanani.
Ubangiji Yace;
“Kuma za mu jarraba ku da sharri da alheri a matsayin fitina, kuma gare Mu kuke komawa.” (Anbiya:35). Bai kamata ga mutum idan ya tsinci kansa a cikin Jarrabawa ta kunci ko talauci ko dusashewar daukaka ko ciwo ya zargi wasu mutane ba. Allah yana jarabtar bawa Sakamakon abin da ya aikata ga ‘Yan uwansa mutane na Alfahari, Dagawa da Girman kai. To shin Ina ma matsayin takawakkali da yadda kaddara?

Tawakkali ga Allah shine abin bukata daga ko wane mutum,
a ko wanne hali ya tsinci kansa.
Cikakken tawakkali shin zuciya ta nutsu ta mika komai ga Allah ta haka za’a samu alkairi da kariyar daga sharri.
Babu wanda ya isa ya baka daukaka ko ya kwaceta sai Allah in dai ka dagara ga Allah hakikani dogaro, Allah zai azurtaka kamar yadda yake azurta tsuntsu da sauran dabbobi.

In gaske ne mutum ya fawwala lamuransa ga Allah, ya yadda da Allah shi yake bada daukaka da daukewarta, to sai a nisanci Kage, zargi, camfi, da tazarta masana’antar da Allah ya baka suna a cikin ta kai aure kai gida kasai babur. Lallai in da kake yanzu haka Allah ya so ya ganka
Ubangiji Yace; cikin Qurani
“Kuma Idan Allah ya shafe ka da wata cuta, babu mai yaye ta, sai shi, idan kuma ya shafe ka da wani alheri, babu mai iya ture falalarsa. Yana samun wanda ya so daga cikin bayinsa da ita, kuma shi mai gafara ne, mai jin kai” (Yunus 107)

[email protected] #sisters & #brothers

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?