Wednesday, 2 January 2019
Ko Me Ya Sa Jama'a Suka Fi Damuwa Da Rashin Auren 'Yan Finafinan Hausa?

Home Ko Me Ya Sa Jama'a Suka Fi Damuwa Da Rashin Auren 'Yan Finafinan Hausa?
Ku Tura A Social Media

Daga Abdullahi Muhammad Maiyama

A duk lokacin da aka bayyana wani aikin alkairi da 'yar fim mace ta yi, sai ka ga maimakon a jinjina mata sai a
dinga sauke sako dake nuna bacin rai game da rashin
yin aurensu.

Wannan fa aiki ne babba, amma mu duba bangare daya
zuwa biyu kawai!

Dukkanin masu nuna bacin ransu game da rashin auren
‘yan fina finan, mutane ne kawai dake son su a fuska, a
mafi yawan lokuta idan har mutum ya zo maka da irin
wannan zance a Inbox, da zarar ka tambaye shi shin kai
za ka aure ta? Amsa daya zuwa biyu zai ba ka. Farko:
A'a, ko kuma ta fi Karfina.

 Amma kuma a haka za ka ga
ya dage a shafukan sada zumunta cewa su je su yi aure,
anya mace na iya auren kanta?

Duk da cewa ba kariya zan bai wa kowannen su ba, lallai illa ce babba macce ta yi wani girma irin na ‘yan shekaru
20 zuwa 30 ba ta yi aure ba, musamman idan har ta sami
miji nagari.

Ya kamata ‘yan finafinai mata ku gane gaskiya ta
hanyar auren mutanen da ke zuwa muku da niyyar aure,
domin mafi akasarin masu kallon finafinaku da kuma
masu nuna muku soyayya a shafukan sada zumunta
mutane ne da ba za su iya aurenku ba. Kun ga irin tasu
soyayya da suke nuna muku ita ce soyayya marar
amfani.

Allah ya ganar damu gaskiya ya bamu ikon aiki da ita.

Domin tuntubar marubuci: 08146697276

Share this


Author: verified_user

0 Comments: