Friday, 25 January 2019
Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari

Home Jirgin kasa: Amaechi ya saka ni a matsala - Buhari
Ku Tura A Social Media
A yau, Alhamis ne shugaba Muhammadu Buhari ya ce MInistan Sufuri, Rotimi Amaechi ya jefa shi a cikin matsala yayin da ya yi alkawarin gina layin dogo da za ta hade yankin Kudu maso Gabashin kasar da Arewa.
Shugaba Buhari ya yi wannan jawabin ne a wurin taron kaddamar da yakin neman zabensa da akayi a cikin filin motsa jiki na Nnamdi Azikwe da ke garin Enugu.
Buhari ya ce abu ne mai wahala gamsar da majalisar zartarwa na kasa su amince da ayyukan layin dogo amma ya ce zai yi iya kokarinsa domin ganin 'yan majalisar sun fahimci muhimmancin gudanar da aikin.

"Amaechi ya yi muku alkawari amma ban san yadda zan cika alkawarin ba. Amma zanyi iya kokari na domin ganin 'yan majalisar zartarwa sun amince da gudanar da aikin," inji Buhari.
Ya ce ba a gabatar wa Majalisar Zartarwa alkawarin da Amaechi ya yi ba inda ya ce zai fi dacewa a bari Majalisar su amince da aikin kafin a bayyana wa mutane.


Shugaban kasar ya mika godiyarsa ga mutanen yankin bisa yadda suka fito kwansu da kwarkwata su tarbe shi kuma ya shawarci su kasance masu kishin Najeriya domin ba su da wata kasar bayan ita.
Ya kara da cewa, "ya zama dole dukkanmu mu hannu hannu wurin guda domin ciyar da kasar mu gaba saboda ba mu da wata kasar bayan wannan."

A baya, Ameachi ya shaidawa 'yan jam'iyyar da magoya bayansu cewar za a farfado da layin dogo na yankin kudu.
Ya ce babban aikin da za muyi shine, "zamu amince da shimfida layin dogo daga Fatakwal zuwa Maiduguri wanda zai wuce Fatakwal zuwa Onitsa har zuwa Awka.
"Na biyun kuma zai bi ta Fatakwal, Umuahia, Enugu, Makurdi da Jos."

Amaechi ya ce, "sauya tsarin rabon arzikin kasa zai yiwu ne idan aka sake zaben shugaba Muhammadu Buhari saboda dan kabilar Ibo ya zama shugaban kasa bayan Buhari ya kammala wa'adinsa."

Rahoto daga :legit.hausa.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: