TASKAR MARUBUTA

IZNAH PART 6 : Labari Cike Da Makirci

IZIAH 6

Anano kuwa har ruwan yayi zafi tana durqushe agurin Saida jafar ya cika Mata bokiti ya sirka yakai Mata qofar bayi takuna ta miqe jiki a sanyaye ta shiga ‘daki ta tube ta fito sum sum tashige bayin.
Duk da tana cikin tashin hankali da damuwar makomar jaririn sosai taji da’din wankan Dan Nan take taji ta’dan warware ajikinta.
Tana gama wankan kafin takai ga fitowa yaron yatashi Nan take ya kara’de gidan da kuka cikin sauri ta janyo zaninta ta ‘daura ta fito
Turus tayi jikinta na saki sbd ganin ba Wanda ya motsa cikinsu kamar basusan da acikin gidan ake kukanba.
Sanyi qalau jikinta yayi Dan kuwa taga tabbas ko barinsa ya zauna gidan baffa yayi bamai qaunarsa.
‘dakin tashige bayan ta aje bokitin hannunta ta zauna kusada yaron Nan itama tafara nata hawayen Dan kuwa tasan daga ita harshi suna tsaka.
Saidataji kukan harya fara sanyashi laushi takai hannu ahankali ta ‘dauke tareda qura Masa Ido Dan Sai alokacin tafara kallon fuskarsa.
Farine sosai Kuma da gani ba lallaine yayi baqi ba duk da dai bazata iya cewa ga fuskar mahaifiyarsa ba sbd komai yafarune cikin duhu..
Numfashi ta sauke ahankali cikin zuciyarta tace,
Allah yasa su hamma su gano gawarta asuturta kodan jaririn.
Sallama aka fara kwadowa a qofar gidan baffa ya kalli qofar da sauri zuciyarsa na ‘dan tsinkewa ya miqe daqyar tareda tattaro ‘yar nutsuwa ya nufi qofar aliyu nabin bayansa.
Murmushin qarfin hali yasaki lokacin dayaga Mal Garba maqwafcinsa yace,
Aa Mal Garba Kaine da safennan.
Cikin ‘yar damuwa yace,
Nine Mal salisu an gari lafiya?
Lafiya qlau Mal Garba ya iyalin?
Alhamdulillah nace ko anji want bayani akan Anano kuwa?
Washe baki baffa yayi cikin qarfin hali yace,
Eh kaga shaf na manta na sanar maka tun a Daren jiyan tadawo Wai Ashe ita da qafa ta qaraso daga can rugar nuhu shiyasa ta iso dare sosai.
Masha Allah Abu yayi kyau dama dai nace ne nazo naji halinda ake ciki Kan 6atan nata Allah ya tsare gaba.
Amin Amin Mal Garba nagode.
Bayan tafiyarsa baffa ya Jima tsaye Yana tunani kafin suka juya suka koma cikin gidan Kai tsaye inna ya kalla yace,
Ki kimtsa yaron ki goyesa duk tsanani Kar kibari agane da akwaisa acikin gidannan.
To tace badan ranta yasoba saidan Bata qetare umarninsa ta miqe ta sake ‘dora wasu ruwan.
Cikin qanqanin lokaci Inna tayi Masa wanka ta gasashi sosai ta ‘debi sabuwar madarar shanu tabasa yasa sosai Nan take yayi luf bacci Mai da’di ya daukesa takuwa goyesa bayanta tasaka hijab bazaka taba cewa akwai ‘da a bayanta ba.
Sai alokacin Anano ta’danji sanyi aranta take Kuma mamakin yanda takejin yaron har tsakiyar ranta.
Kamar jira ake Inna ta goyesa Nan take jama’a suka fara zaryar zuwa barka da dawowarta dakuma ganinta da’akayi.
Su ubaidah sunxo Nan suka hauta da fadan tafiyarta datayi Bata tsaya musu ba.
Itadai murmushin yaqe kawai take musu
Koda suka tambayi kumburin fuskarta da Jan idonta cemusu tayi batai bacciba ahanya qunama ta cijeta.
Sosai suka tausaya Mata duk da sun fahimci kaman Bata cikin walwala hakanan suka qarashi firarsu suka tafi.
Su Yusuf kuwa duk iya bincikensu Basu ga wata gawaba haka suka dawo suka sanarwasu baffa qarshe dai aka tattara zancen aka aje Sai bayan kwana biyu tukuna a yanke shawarar abinyi.
Tunda tadawo kusan komai ya canxa Mata ba kamar da ba da kowa gidan keji da ita kamar su lasheta Amma yanxu kaf yayunta iyakacinsu da ita ta gaidasu idansunga dama su amsa idan basuga damaba su qyaleta baffa da jafar ne kawai ke kulawa da ita Sai Usman idan yaga dama shima,
Inna kuwa kadaran kadahan ga baffa dayasata kulada jaririn Dole badan tasoba.
Sosai hankalin ananon hankalinta yafara ‘dan kwantawa sbd ganin anbar zancen saigashi Randa sukai sati ‘daya kwatsam zancen yafara fita Wai akwai jariri agidan Nan maganganu suka fara yawo hankalin baffa yafara tashi musamman da zancen yafara yaduwa Wai ‘dan na Anano ne tunda dai ba Wanda zai haihu a gidan.
Zaune suke a tsakar gida yau duk sunyi jugum jugum bamai magana Sai Inna daketa aikin Kai kawon girkin dare datakeyi Anano kuwa tana zaune tana yiwa Inna wanke wanke jiki a sanyaye sbd tun Daren jiya taji hirar Inna dake bawa baffa shawarar akai yaron gidan Mai gari ace tsintarsa akayi.
Cikin sanyin murya baffa yace,
Idan muka kaisa mukace tsintarsa mukayi kenan mun bada damar daza’a yarda da zargin da ake Mana sbd zaaga meya Hana tun farko mukaisa Saida aka ganomu,
Kawai dai na yanke shawarar aikasa can binni gidan marayu kamar yanda Yusuf yace tun farko.
Da wannan tunanin ta kwana ta tashi sosai taji hankalinta yatashi sbd tausayinsa dakuma qaunarsa dake maqale aranta.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?