Tuesday, 22 January 2019
IZNAH Part 1 - Labari Cike Da Makirci

Home IZNAH Part 1 - Labari Cike Da Makirci
Ku Tura A Social Media


IZNAH PART 1

Bismillahir-rahmanir Raheem.
Dattijo ne 'dan kimanin shekaru hamsin zuwa sama fari sol dashi Wanda kallo 'daya zakayi Masa ka tabbatarda cikakken bafulatani ne,
Zaune yake kan tabarma a tsakar gidansa Yana kallon Mai 'dakinsa cikin farin cikin yanda take gyaran shinkafar daya siyo Dan kawai a girkawa 'yar gaban goshinsa abincin tarbanta na dawowa daga makaranta data share watanni acan.
Da sallama wani 'dan madaidaicin saurayi yashigo hannunsa riqeda baqar Leda ya miqawa innarsu Yana cewa,
Baffa wlh yau kifi yayi wuya daqyarma nasamo wannan 'din sauran abari gobe da sassafe kafin su iso nakoma nagani ko za'a samo.
Fuska cikeda annuri baffan yace,
Ba komai jafar wannan 'dinma zai Isa tunda goben nace aliyu ya Kama kaza biyu ya yanka Mata taci iya cinta.
Girgixa Kai inna tayi cikeda mamakin baffan akoda yaushe da baya iya danne fificin soyayyar _*ANANO*_ acikin ransa duk garin ansan soyayyarta daban take aransa akan sauran 'yayansa.
Baffa salisu shine cikakken sunansa Kuma haifaffe Dan asalin qauyen 'danja qarqashin wata qaramar dake cikin jahar yola.
Baffa nada Mata 'daya da 'yaya biyar ha'du maza Sai 'daya mace Wadda 'yan biyune aka haifesu Amma husainar takoma tun kafin suna Sai aka barta da sunanta na _HASSANA_ Amma suna kiranta da _ANANO_ ma'ana hassana da fillanci.
Anano itace auta Kuma itace qaramarsu kasancewar ba'a haifetaba Saida duka yannenta suka girma Sai yazamto kowa gidan ji yake da ita musamman baffan daya 'dauki tsananin so da qauna ya 'dora Mata kasancewar ita ka'daice yarinya qarama a gidan Dan tuni yannenta suka Zama samari.
Baffa nada arzikin dabbobi daidai gwargwado hakama yanada gonarsa dayake noma duk shekara shida 'yayansa.
Kaf qauyen Babu Wanda yayi karatun Boko Banda noma da kiwo Sai kuwa karatun addini,
Yusuf shine babba Kuma mai 'dan hakr saidai idan yafara fa'da to yanada wuyar saki,
Aliyu shine Mai bin Yusuf Wanda shikuma akwai fa'da da zafin Rai musamman idan aka ta6asa shiyasa kowa bai cika shiga sha'aninsaba,
Sai Usman wanda Shima akwai rashin ji da fa'da musamman akan anano dayake ganin tafara iya rashin kunya sbd sakarcin shagwa6a.
Jafar shine Mai sanyi da hkr acikinsu musamman akan anano dayake tsananin jida ita shima duk da dai kaf 'dinsu suna tsananin sonta Amma tafi shiri dashi matuqa danshi har dandali yake kaita tayo kallo sudawo gida.
Tunda ta taso take Jin son karatu aranta Wanda kullum firarta kenan da baffanta Wanda yayi niyya tareda alwashin kaita makaranta saigashi cikin ikon Allah aka turo masu fa'dakarwa akan karatun Boko qauyen shine mutum na farko daya yarda 'yarsa taje kafin aka samu wasu qalilan Suma suka amince Nan take aka fara Shirin makaranta suka fara zuwa.
Suna gama primary acikin qauyen suka wuce bording secondary School dake can cikin babban garin adamawa.
Tunda tafara zuwa makarantar idanuwanta suka qara bu'dewa musamman sbd dama can anano akwai tsiwa da ilimin iya fa'dar baqar magana Wadda ba'a fa'da Bata mayarba Koda kuwa mutum waye.
Wannan hutun dasuka koma sun Dade Dan kuwa Saida suka share kusan wata biyar acan kafin suka fara shirye shiryen dawowa Wanda sun gama karatun kenan.
Tunda jafar yaje yadawo yasanarda dawowarta ta gamo makaranta baffa da'di ya ishesa yafara shelar Ananonsa ta gamo karatu zata Zama babbar likita Mai Duba mutane.
Nan take gari ya 'dauka musamman ma da'akaji Wai tazamo likita.
Shiri na musamman yasa ayi na tarbon Anano tareda murnar dawowarta Dan tuni aka fara zuwa tayasa murna tun kafin ta qarason.
Anano farace tas tamkar 'yan gidansu saidai kaf tafisu kyau kasancewarta mace,
Ayanxu data kammala secondary 'dinta tanada shekaru goma Sha bakwai.
Koda dare yayi duk wani toye toye da gashe gashen kifi angama sbd ba abinda tafiso kamar gashashen kifi da albasa tun tana qarama shiyasa harshi Saida baffa yasiyo aka gasa Mata.
Washe gari tunda safe yasa inna ta share ko Ina tareda 'dora girkin shinkafa harda miyar tumatir Wanda takanas sbd ita yabada kudi aliyu yaje birni yasiyo shinkafar Dan adafa Mata.
Koda inna tagama aikin komai 'daki takoma ta kwanta sbd ciwon kan daya saukar Mata lokaci 'daya gashi Rana hartayi yamma na nemanyi Amma shiru 'yan makarantar Basu isoba.

Share this


Author: verified_user

1 comment:

  1. Enter your comment... TO FATAN ALKHAIRI A GARE KU MARUBUTA, ALLAH YA QARA BASIRA.

    ReplyDelete