Thursday, 10 January 2019
Hajiya Rukayya Matar Aure Ce Kuma Ita Ce Mahaifiya Ta, Cewar Mustapha Atiku Abubakar

Home Hajiya Rukayya Matar Aure Ce Kuma Ita Ce Mahaifiya Ta, Cewar Mustapha Atiku Abubakar
Ku Tura A Social Media
Hoton da wasu bata gari ke yadawa da sunan 'yan Jaridar Soshiyal Midiya wanda ya ke nu na dan takarar shugaban kasa Alh. Atiku Abubakar, ya rungume wata mata wannan matar ba kowa ba ce Illa mahaifiyata, Inji Mustapha dan cikin Atiku Abubakar.

Mustapha, ya kara da cewa duk da yake samun kafafen yada labarai na zamani sun kawo cigaba mutuka amma wasu suna amfani da ita wajen cin zarafin jama'a kuma ina amfani da wannan dama in shaida ma masu irin wannan ta'asa cewa duk abin da wani zai basu dan su ba ta wani to su tuna za su koma ga Allah.

Ya cigaba da cewa nasan duk wani dan halaka uwa da uba ne abin tunkahon sa kuma in dai kai musulmi ne ko kirista ba za ka taba yadda a ci mutuncin Aure da kai ba saboda Aure ne asalin duk wani dan halak.

Ka iya tunawa cewa in mahaifiyar ka ce ya za ka ji? Duk da dai nasan Kayode Ogundumasi, bai san me a ke kira Aure ba amma abin kunya ne a ce musulmi ne ke yada irin wannan karya da kage gami da cin mutuncin Aure.

In baku manta ba dai a kwanakin nan wasu sun yi ta yada wannan hotunan suna cewa wai wannan wata 'yar siyasa ce kuma Shugabar Mata a wata jiha alhali mahaifiyata ba 'Yar Siyasa ba ce Inji shi.

Me za ku ce jama'a?

Share this


Author: verified_user

0 Comments: