Friday, 11 January 2019
Guzurin Ma'aurata Hanyoyin Gamsar Da Mai Gida A Lokacin Jima'i

Home Guzurin Ma'aurata Hanyoyin Gamsar Da Mai Gida A Lokacin Jima'i
Ku Tura A Social Media
Daga Farida Muh'd

Farko yadda za ki fara bi wajen gamsar da mijinki shi ne nuna masa shauki da zumudin son yin jima’i, kada ki nuna jin kunya domin nuna masa zumudi wajen saduwa zai ba shi damar shirya kansa da kuma yin zumudi shi ma, wanda idan haka ta faru kin taka wani mataki na gamsar da shi domin kin motsa masa sha’awarsa.

Yayin jan hankalinsa ki yi kwalliya da ado, ki fesa turare mai sanya shauki, sannan ki rika yauki da shagwaba da kuma kisisina.

Hanyar jan hankalin miji ta hada da rausayar da jiki, sanya tufafin da za su fitar da sura don hakan ya kara janyo hankalin miji. Murmushi, yin kalamai cikin tausasa murya, wani lokaci mai cike da sigar rada tana haifar da motsuwar sha’awar mazaje. Yin kalaman barkwanci, yin wasa ga miji da sauransu.

HANYA TA FARKO

A kullum ko lokaci-zuwa-lokaci ki rika amfani da sabbin hanyoyin yayin jima’i wajen gamsar da mijinki, kada a kullum ki rika amfani da salo daya yayin kwanciya hakan zai sa ki gunduri mijinki. Kada ki manta jima’i kamar cin abinci ne, mutum yakan so ya samu canjin abinci ko dandano, to haka batun jima’i yake, yana bukatar salo-salo don a samu dandano daban-daban. Amma sai ka ga wadansu matan sun kwanta kawai ba tare da yin wadansu dabarun da zai kara wa mijinsu karkashin son yin jima’i har ya samu gamsuwa ba.

HANYA TA BIYU

A lokacin da aka zo jima’i yana da kyau ki karfafa wa mijinki gwiwa, ba kamar wadansu matan da suke zama ko oho ba, ba ruwansu da karfafa wa mijinsu gwiwa ba, idan ya samu karfin gwiwar gamsar da ku, to shi ma zai samu gamsuwa domin ya samu yakinin cewa ya gamsar da ke.

HANYA TA UKU

Yin wasanni ba wai sai lokutan da za a sadu ba, ya kama ki rika yi wa mijinki wasanni a wadansu lokutan da kika lura yana cikin nishadi. Za ki iya masa wasannin ne ta hanyar shafarsa, sosa gashin kansa, tattaba yatsunsa da lankwasa su, inda wani lokaci za ki rika zungurarsa kadan. Yana da kyau ki rika ba shi labarai masu ban dariya da sanya nishadi, wani lokaci ki rika zolayarsa, yanayin yadda zai rika sake jikinsa gare ki zai nuna miki yana samun gamsuwa. Ta wannan hanyar ma za ki iya isar da sakon nuna son jima’i ba tare da bayyanawa da baki ba.

SAKO ZUWAGA UWAR GIDA

Zan yi miki bayanin wadannan wurare 9 don su kasance wani sirri a wurinku da za ki rika sarrafa mijinki yayin jima’i cikin ruwan sanyi.

Wadannan wurare suna dauke da jijiyoyi wadanda kai tsaye suke aika sako zuwa kwakwalwa cikin kankanen lokaci.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: