Tuesday, 22 January 2019
Gaskiyar Labari : Wasan Kwaikwayon Mayar Da Mace Kura A Kano

Home Gaskiyar Labari : Wasan Kwaikwayon Mayar Da Mace Kura A Kano
Ku Tura A Social Media

An gayyato mai wasa da Kura ne daga jihar Katsina domin shirya fim. A fim din za a nuna wata mata na kuka an mayar da 'yar uwar ta Kura.

Wannan ya sa mutane suka dauka gaskiya ne ba shirin fim ba. Daga nan aka mayar da wasan kwaikwayo gaske. Sohiyal Midiya kuma ta kama da wuta an mayar da Mace Kura a jihar Kano.

idan ba don Allah Ya sa mai wasa da Kura na da sauran kwana ba, da tuni an babbake shi da ransa. In banda an kai shi wajen 'Yansanda sun gano gaskiya.

Godiya ga Dan jarida Abba Ibrahim Gwale da ya  bibiyi labarin, ya je ofishin 'Yansanda na Gwale ya tabbatar da gaskiyar labarin. Mai son ganin bidiyon ya duba shafinsa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: