Wednesday, 30 January 2019
Faifen Bidiyon Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar

Home Faifen Bidiyon Ganduje: Kotun Shari'a tayi watsi da karar da aka shigar a kan Jaafar Jaafar
Ku Tura A Social Media

Wata babban kotun Shari'ar musulunci da ke zamanta a Goron Dutse a jihar Kano tayi watsi da karar da wani Dalhatu Shehu ya shigar a gabanta inda ya ke neman babban Editan Daily Nigerian, Jaafar Jaafar ya gurfana a gaban kotun a kan wallafa bidiyon da ake zargin rashawa Gwamna Abdullahi Ganduje ya ke karba.

A watan Oktoban 2018 ne Daily Nigerian ta wallafa wasu faya-fayen bidiyo da ke nuna Gwamna Ganduje ne ke karbar cin hanci na daloli daga hannun wani dan kwangila.

A wata Nuwamban 2018 ne Ganduje ya shigar Jaafar Jaafar kara inda ya ke neman a biya shi Naira Bilyan 3 saboda wai 'yadda bidiyon karya da niyyar cin mutuncin gwamnan da bata masa suna.

Duk da cewa Gwamnan ya shigar da kara a babbar kotun da ke jihar, wani lauya da ke biyaya ga Ganduje mai suna Dalhatu Shehu ya shigar da wata karar a babban kotun Shari'ar a makon da ta gabata.

Da farko wanda ya shigar da karar ya ce akwai bukatar Jaafar ya gurfana a gaban kotun ya yi rantsuwa da Alkur'ani mai girma a ranar 29 ga watan Janairu.

Amma a lokacin sauraron karar ya yi a ranar Talara, Alkalin kotun, Mohammed Kademi ya yi watsi da karar inda ya ce wanda ya shigar da karar ya janye.

Lauya mai kare Jaafar, Audu Bulama-Bukarti ya nemi kotu ta bashi cikaken bayanin yadda aka janye karar kuma kotun ta amsa wannan roko nasa.

Sources: Fb/Nijeriyarmu A Yau

Share this


Author: verified_user

0 Comments: