Sunday, 27 January 2019
Da duminsa: IGP Adamu ya yiwa dukkanin mataimakan Sifeta Janar ritaya

Home Da duminsa: IGP Adamu ya yiwa dukkanin mataimakan Sifeta Janar ritaya
Ku Tura A Social Media


Wata majiya ta shaida cewa, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda Muhammed Adamu ya yiwa dukkanin mataimakan Sifeta-Janar guda bakwai na rundunar ritaya - Wannan ritayar ta faru ne a yammacin ranar Lahadi, kuma za a sanar da ita a hukumance daga bisani, kamar yadda rahotanni suka bayyana - Shima a lokacin da ya zama Sifeta Janar, Mr Idris ya yiwa sama da DIG da AIG ashirin ritaya domin basu damar kafa tsarin shugabancinsa Wata majiya daga rundunar 'yan sanda ta shaidawa jaridar Premium Times cewa, Sifeta Janar na rundunar 'yan sanda Muhammed Adamu ya yiwa dukkanin mataimakan Sifeta-Janar guda bakwai na rundunar ritaya, wadanda kuma sun fi sa matsayi a cikin aikin. Mataimakan Sifeta Janar na rundunar da ritayar ta shafa sun ahada da Maigari Dikko, da ke kula da sashen kudi da mulki da kuma Habila Joshak, da ke kula da ayyuka. Sauran biyar din sun hada da Emmanuel Inyang, mai kula da sashen watsa labarai da sadarwa; Agboola Oshodi-Glover, sashen shigo da kaya da dabaru; Mohammed Katsina, sashen bincike da tsare tsare; Sani Mohammed, sashen bunkasa horo ga jami'ai; da kuma Peace Ibekwe-Abdallah, sashen kwararru kan binciken laifukan ta'addanci na gwamnatin tarayya. .

Wannan ritayar ta faru ne a yammacin ranar Lahadi, kuma za a sanar da ita a hukumance daga bisani, kamar yadda rahotanni suka bayyana. Sai dai duk wani yunkuri na tuntubar kakakin rundunar, Frank Mba ya ci domin ya yi tsokaci kan lamarin. Mataimakan Sifeta Janar na rundunr sun kama aikin dan sanda ne tun kafin Mr Adamu ya kama, wanda ya zama Sifeta-Janar na rundunar a ranar 15 ga watan Janairu bayan da tsohon Sifeta Janar Ibrahim Idris ya yi ritaya da shekaru 60. Yiwa manyan jami'an rundunar ritayar dole, bin wani tsari ne na rundunar, wanda ya tilasta yiwa duk wasu manyan jami'an rundunar ritaya a duk sanda aka ce wani karamin jami'i na rundunar ko wanda yake kasa da su a mukami ya samu matsayi na shugabantar rundunar. Shima a lokacin da ya zama Sifeta Janar, Mr Idris ya yiwa sama da DIG da AIG ashirin ritaya domin basu damar kafa tsarin shugabancinsa.

Rahoto Legit.ng

Share this


Author: verified_user

0 Comments: