Labarai

Buhari ya kalubalanci yan Najeriya su tona asirin duk wani barawo dake gwamnatinsa

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kalubalanci yan Najeriya dasu tayashi kama duk wani barawon gwamnati dake cikin gwamnatinsa ta hanyar fallasashi tare da bayyana hujjojinsu akansa don ya dauki matakin daya kamata.
Legit.ng ta ruwaito Buhari ya bayyana haka ne a yayin taron sauraron jin ra’ayin al’umma mai taken ‘The Candidates’ ma’ana yan takara, daya gudana babban birnin tarayya Abuja a daren Laraba 16 ga watan Janairu wanda gidauniyar Mac Arthur, NTA da kamfanin DARIA suka shirya.
Buhari a yayin tattaunawar
Buhari ya bayyana haka ne yayin da yake amsa wata tambaya da aka jefa masa dake nuni da cewa wai yaki da rashawa da gwamnatinsa take yi ya karkata ne kawai ga wani sashi na yan Najeriya, amma ba’a taba yan jam’iyyar APC, sun zama shafaffu da mai.
Jagoran shirin, Kadaria Ahmed ta yi nuni da misalin tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal, wanda shugaba Buhari ya saukeshi daga mukaminsa sakamakon cin rashawa, amma har yanzu ba’a gurfanar da shi gaban kotu ba.
Jin hakan tasa Buhari yace: “Gaskiya ba ayi min adalci ba, bana jin akwai wani jami’in gwamnatinnan da aka tabbatar mana da cewa ya saci kudinsa kuma mun bashi kariya, amma dole ne mu yi takatsantsan, jama’a su taimakemu da bayanai gamsassu, kamar su lambar asusun banki, sunayen kamfanuwa da kuma kwangilolin da aka sace kudin dasu.
Idan muka samu wannan, mu kuma zamu mika ma EFCC da ICPC su shigar dasu kotu bayan sun gudanar da cikakken bincike, anan kuma dole ne mu kyale tsarin shari’a tayi aikinta, babu yadda za’ayi mu yi yaki da rashawa kamar yadda muka yi a mulkin Soja, Dimukradiyya bai bada wannan dama ba,
“Kamar tsohob sakataren gwamnatin tarayya, mu da kanmu muka sallameshi, kuma a yanzu haka maganan na gaban EFCC, kuma tuni mun bada umarni ga EFCC da ta gurfanar da shi gaban kotu da duk mutanen dake irin wannan laifi a gaban EFCC.” Inji shi.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?