Saturday, 26 January 2019
BABI NA BIYU : SAWUN BARAWO !

Home BABI NA BIYU : SAWUN BARAWO !
Ku Tura A Social Media
SAWUN 'BARAWO
Noorieyyaah.
(2)
To Lubbatu Maitafsir this page is solely dedicated to you, thank you for your love and time towards this work.
You are utterly amazing babe, i heart you loadz.💖
***
"Kakus wai meke damun ki neh? Tun dazu na ke faman doka sallama but da'alama hankalin ki baya tare da mutanen nigeria"
Ya ida maganar cike da son ganin ya sanya ta nishadi, diba da yanayin da ta Sanya kanta tun bayan afkuwar al'amarin da ya dagula dukkan lissafin mutanen gidan.
"Me kuwa"
Ta bashi amsa cike da k'osawa, domin kuwa tun faruwar al' amarin da ya afka wa gidan nasu take jin haushin kowa na ilahirin gidan. A ganin ta tsabar son kai neh da k'iyayya ya saka sukai wa yaron kirki (safwan) wannan sharrin.
"Kuma ka tashi salin alin kabar mani d'aki, bana buk'atar sake sanya ka a idanuwa nah"
Ta d'auke kan ta tana faman ciccin magani, alamar daza ta tabbatar maka da cewar ran ta ba k'aramin suya yake bah.
"Toh! Ni kuma kakus menayi?, amma dai koma meke damun ki kamata yayi ki zayyana mana, bawai kiy ta nuk'ura ba kina huhhura hanci"
Sanin me zai biyo baya yasaka shi mik'ewa da hanzari yayi hanyar waje, tun kafin yaji saukar kofi a goshin sa.
"Ai da ka tsaya, fitsararre mara kunyah, da gangan ake ganin laifin yaron kirki bayan kai d'in nan kafi shi shed'anci" "macuta kawai"!
Dariya salim yacigaba da kwasa a yayin daya tsinkayo amsar da take bashi, hakan yasa ba tare da ya lura ba suka ci karo da hajiyar su, a yayin da take sanyo kai daga corridor d'in da zai sadaka da madafin gidan(kitchen).
"Kai kuma lafiyan ka kake dariya kai kad'ai, gashi har kana shirin kai ni k'asa"
"Afuwan hajjaju, ni da kakus neh, kin san halinta in tana jin haushi, Ba kya ganin abin da ya faru neh yasaka ta cikin halin da take ciki? Nabila fa jiya har waya tayi mani wai ko abincin kirki bata ci sai tunani da ta saka a gaba".
Ajiyar zuciya hajiyan ta saki cike da sarewa da al'amarin na innah, domin kuwa ba irin faman da ba tayi da ita akan ta kwantar da hankalin ta komi zai zo k'arshe amma hakan ya gagara.
Babban abinda yafi d'aga mata hankali shine, ganin har yau kwana kusan takwas da afkuwar lamarin tak'i ta ce komi, in banda hora su da take faman yi da idanuwan ta, ita a dole sharri a kayi wa shalelen ta.
"Ban san ya zanyi da inna ta fahimci gaskiyar al'marin nan ba. Sabida Allah ramlah ba yarinya bace ballan tana ace bazata iya shaida wan da yai mata wannan aika aikar ba, besides ku kunfi kowa sanin cewar ko giyar wake ta sha ba ta isa ta danganta lamarin ga safwan ba matuk'ar ba shi d'in ta gani ba. "
Ta numfasa kana ta cigaba" For God's sake ta yaya ma za'a ce sharri akai masa? Bayan kowa yasan munanan halayen shi na kasantuwar shi mutumin banza, nayi imani da Allah tun da ramlah ta tabbatar mana da cewar shi neh, toh kuwa babu tan tama shi d'in neh"


Saleem d'inne yai shiru cike da tu'ujjibin abin, haka nan kuma zuciyar shi ta kasa k'arya ta zancen na ramlah. Tabbas babu ma wata tantama safwan dinne ya aikata fyaden, domin kuwa a kafatanin gidan na su babu d'an akuy irin safwan d'in.
"Amma hajiya ta yaya kuke ganin yiwuwar auren nan? Kun fi kowa sanin halin safwan da shegiyar kafiya, idan har yace yes babu wanda ya isa yasaka shi yace No!"
"Ta yaya kuke ganin zai amince da auren nan tun da har ya rantse cewar be yi"?
Sauke ajiyar zuciya hajiyan ta yi cike jimami, haka nan kuma ba tare da ta k'ara cewa komi ba ta juya ta nufi hanyar dakin innar.
Da sallama hajiyar ta shiga bedroom d'in na inna, inda dak'yar innar ta bude baki tamkar mai ciwon baki ta amsa can k'asan mak'oshin ta, shima amsawar da tayi don yazame mata dole neh, da bata ansa ba.
Ba tare da nuna damuwa ba hajiyar ta nemi d'aya daga couch d'in dake girke a d'akin ta zauna gami da fuskantar innar dake kishingid'e bisa makeken gadon ta, lokaci guda kuma tana amsa sak'on kallon banzar da innar keh wurgo mata.
"Inna barka da safiya, da fatan kun tashi lafiya"?
Batare da ta kalli gefen ta ba ta juya kai gami da cewa "Garas na ke, ko kuna tunanin don kun had'a baki kun yi wa d'an tahalikin Allah sharri zai saka nadai na  rayuwa ta kamar kowa" ?  Tacigaba....
"Burin ku dai ya cika kun b'ata man rai, amma bakuyi nasarar san ya zuciya ta bugawa ba,sanin cewar wanda ake tsiyar don shi yasan maganin ku"
Shiru hajiy tayi tana faman godewa Allah bisa wannan ikon Allahn da take gani daga surukar ta ta. Jin innar tayi shiru ya sanya ta fahimtar cewar ta gama fad'an, hakan yasa ta fara da ban hak'uri ga innar domin ganin ta ci nasarar karkato da hankalin innar ta fahimci cewar ba sharri akai wa safwan d'in ba.
Katse ta innar tayi jin ta dage tana koro mata bayanin bogi, eh mana a wajen ta ai bayanin bogi neh, domin kuwa ko da me suke yawo bazata tab'a yadda a tilas tawa yaron kirki auren wacce be so ba.
"Saratu kin san Allah kin ishe ni, kin cika mani kunnuwa, shi wanda ake abin ma don shi kun sake sanya shi a idanuwan ku tun ranar?Eyeeh? Nace kun sake sanya shi a ido?"
Da sauri hajiya ta girgiza kai alamun ah ah, hakan yasa ta dora da cewa "Kuma inna ai kunfi kowa sanin safwan, haka nan ma inya bushi iska sai afi sati be lek'o gidan nan ba, bai kama ta ku da mu ba"
Sai da ta wurgo wa hajiyar harara kana tace "Kyace haka mana, tun da bakya k'aunar ganin sa, abin haushi kuma a rashin k'aunar tashi ake k'ok'arin k'ak'aba masa k'ajaga"
Ta numfasa "In ban da rigima ma irin taki saratu ina yaron kirki ina wannan bak'ar d'iyar taki me kama da an d'aura wa muciya zani? Wannan ai zalunci neh mai lasisi ku ke shirin yi"  Mtsw ta ja tsaki cike da jin haushi mabayyani.
Dariya maganar ta inna ta baiwa hajiyan, sai dai gudun janyo wata maganar ya sanya ta boye dariyar a ran ta, ita dai fatan ta innar ta fahimce ta, ta gane cewar shi dai shalelen nata da bata so a fad'i laifin sa shine yai aika aikar da ta wargaza farin cikin gidan.
"Naji sai ki tashi ki tafi sai na kara tabbatarwa daga bakin yaron kirki, cuta ce dai ai an gama cutar shi, wannan irin sharri ko zamanin jahiliyya albarka". Cewar innar.
"Toh ai shikenan inna, ni dama fata na ku fahimce ni, abinda kawai nake buk'ata a wajen ku kenan, na kuma gide da sauraro na du kuka yi, Allah ya k'ara girma da nisan kwana"


Tab'e baki innar tayi, da'alama wannan karon batai maraba ba da jin addu'ar da ta fi son ji a koda yaushe, hakan yasa ta k'ara da juya k'eyar ta gefe, nuni da cewar ba'a burge ta ba.
***
"Ungo nan danno mani lambar yaron kirki"
Ta mik'a wa nabila wayar ta, wacce shigowar ta kenan domin kawo wa innar abincin ranar ta.
Sai da ta sami guri ta zauna kana ta amshi wayar tana mitar shikenan za'a tattago masu almasifatu yau.
"Ungo nan" inna ta jefo mata dak'uwa.
"Zakiyi abinda nasaka ki ko zaki tsaya yi mani alayeh, ai dama yaron kirkinne maganin ku a gidan nan"
Ta zunburo baki gaba gami da cewa "Allah sai in fasa kirawo maki shi, daga taimako zaki hauni da fad'a" ta ida zancen tana kanga wayar a kunnenta.
"Yoo kakus ai babu ma kud'i a wayan naki, kekam sai mutum ya rasa yaushe kike cinye katin wayar taki bayan ko iya danno lamba ba kiyi ba."
"Zancen banza, ni zakiy wa shak'iyanci? Ko dazu sai da na baiwa Khalil ya duba mani, ya kuma ce akwai wajen d'ari biyu da sittin a ciki, me kika gaya man yanzu? " Ta ida maganar tana dak'una fuska, a dole za'a raina mata wayo.
"Nidai bara in kira maki shi da tawa, coz ni ba gane zancen nan da kike mani nake ba, bayan ni ban ga komi cikin wayar taki ba, gaddamar ki har k'ule ni take wallahi"
"Mtsw fitsararriya kema fitsarar zaki mani? Allah dai yabaku sa'a, zaku gane kuren ku in safwanun yazo."
Da sauri nabilan ta matsa gefen ta tazauna tana buga yak'e "Haba ke kuwa kakus daga wasa? Keh ba ki san wasa ba dad'i na dake kenan" ta k'arasa maganar tana rungumo innar, sanin irin mugayen sharrukan da innar ka iya ja mata idan yaya safwan d'in yazo, sannan fad'in abinda zai biyo baya ma b'ata baki neh.
"Yauwa gashi nan tana ringing"
Take innar ta hau buga murmushi kai kace wani albishir akai mata.
"Ai nasan hali dama ubanwa ya haife ka ya safwan ya d'auki kiran ka a kiran farko" Mtsw taja tsaki cike da gajiya da halayen yayan nata.
"Yawwa hello ya safwan, au assalamu alaikum this is nabila mainasara on the line" sanin bazai tab'a tanka maka ba matuk'ar ba ka fa'di sunan ka ba yayin da ka kira shi ko uban waye kai kuwa.
"Mainasara Safwan, how may i help you"? ta tsinkayo muryar shi cike da kasala yana tambayar ta, hakan kuma bai bata haushi ba sanin yanayin sa ne a hakan ako da yaushe.
"Keh zanci uban ki fa, baki da abin fad'a neh kike b'ata man lokaci"?
Da sauri ta manna wa inna wayar a kunnen ta, ganin yana shirin jefa ta cikin black list d'in sa na yau d'in.
"Alo..... Alo... Yaron kirki kana jina"?
"Oh shiiiiiit" ya fada can k'asan mak'oshin sa.
"Sweetheart ya aka yi neh?"
"Menene ma ba'a yi ba safwan, sabida Allah ina ka shige kadena lek'o gida? Haba yaron kirki duk dai nasan cuta ce an riga da ancuce ka, da aka k'ala maka wannan sharrin, amma ai ni ban yarda da su ba, kuma ina nan zan ga wanda ya isa yai maka dole"
"Alo yaron kikrki kana jina"?
"Ina jin ki sweet heart, ki manta da zancen nan yawa kike"
"Wane yawa a nan, mahaifiyar ku na nan na ta shirye ahiryen d'aura maka aure da wannan figaggiyar yarinyar......"
"What! Shiiit.... Shiiit... Wai kina nufin hajjaju bata bar zancen nan ba? Upon all the damn warning i gave them"? Ya katse innar cike da bala'i a muryarshi.
"Oho ni dai ba gane turancin nan naka nake ba kasani kuma, abinda na ke so da kai kazo gidan yau ina son ayi ta tak'are."
"Ki bani rabin awa ina tafe, i fucking dunno why hajjaju ke son shigar mani hanci da k'dundune  for God's sake'! Wallahi in basuyi hankali da ni ba sai na yaga banzar yarinyar nan into pieces, shegiya mai kama da kazar mayu"
"Ah ah yaron kirki inka yaga ta kuma sai ka k'ara wa kan ka laihi ai, ka dai zo musan abin yi."
"Forget kawai kakus, zanci  uban yarinyar nan, ko uban me zan ci da shegiya, ko nonuwan kirki ba ta da su balle akai ga batun ass"
Da sauri inna ta datse kiran tana k'ara jinjina irin rashin kunya ta safwanu, a ranta kuma tana mai fatan shiriya a gare shi.
"Je ki ki tanadar wa yaron kirki abin da zai ci gashi nan tafe"
Warce wayar ta tayi tafice daga d'akin tana mai zumburo baki gaba, da kuma fatan Allah ya jefo abin da zai hana ahi zuwa gidan. "Haba ina ma amfanin masifaffe"
***
Lemme take a breath here sweeties.
Atleast i've tried ai, in this era of fasting, ko
kuwa?
Nasan dai duk kunsan azumin banan nan wa ne
yaro? 😂.
And don't forget to share, vote and comment.
Asha ruwa lafiya.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: