Friday, 4 January 2019
Ba Zan Bar Bayern Munchen Ba –Lewandoski

Home Ba Zan Bar Bayern Munchen Ba –Lewandoski
Ku Tura A Social Media
Tsohon dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Brussia Dortmund kuma dan asalin kasar Poland, Lewandoski wanda yanzu haka yake wasansa a Bayern Munich ya ce shi yanason gama buga wasansa ne a Bayern Munich.
Dan wasan mai shekaru 30 ana dangantashi da shahararriyar Kungiyar Kwallon Kafar nan ta Real Madrida, sai dai yace shifa zai gama wasansane kungiyar da yake bugawa wasa wato Munich.
Sauran kungiyoyin kwalkon kafan da suke nuna sha awarsu ta daukan wannan dan wasa sun hadar ga kungiyoyin Chelsea da Manchester United da AC Millan da kungiyar kwallon kafa ta kuma Paris Saint-Germain.
Da farko ana ta rade-radin cewa a karshen kakar wasannan ce dan wasan zai bar kungiyar ta Munich amma yanzu maganar ta sauya zane inda ya jaddada zamansa a kungiyar kuma yana fatan gama kwallonsa anan.
Lewondowski ya ce “akwai damar rmaki dana samu sosai a zaman danayi a Bayern Munich kuma har yanzu kwantaragina bai kareba sai a shekara ta 2021, saboda haka ba zan bar Munich ba tunda har yanzu Bayern Munich ce a raina”.
Dan wasan dai yakasance daya daga cikin jigo a kungiyar ta Munich inda a kowacce shekara yake zura kwallaye a raga kuma kawo yanzu yafi kowanne dan wasa cin kwallo a gasar cin kofin zakarun turai.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: