Friday, 18 January 2019
Atiku Abubakar Ya shiga Amurka (Kalli Hotuna)

Home Atiku Abubakar Ya shiga Amurka (Kalli Hotuna)
Ku Tura A Social Media
Tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya isa kasar Amurka a yammacin ranar Alhamis.
Kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Twitter, ya je kasar ne domin tattaunawa da jami'an kasar da kuma 'yan Najeriya mazauna kasar.

"Yanzunan na sauka a birnin Washington D.C domin ganawa da jami'an gwamnati da kuma 'yan Najeriya mazauna kasar da kuma yan kasuwa."


Just arrived Washington D.C for meeting with US government officials, Nigerians living in D.C metropolis and the business community. -AA pic.twitter.com/EafM47B83A — Atiku Abubakar (@atiku) 17 Janairu, 2019


 Tsohon mataimakin shugaban kasar ya samu rakiyar shugaban majalisar dattawan Najeriya Bukola Saraki, wanda shi ne Darakta Janar na kamfe dinsa.
Wasu na zargin tsohon mataimakin shugaban kasar ne da kasa zuwa Amurka saboda zargin da aka ce kasar na yi masa na cin hanci da rashawa.
Zargin da ya sha musantawa a lokuta da dama inda ya bayyana cewa babu wanda ya taba kama shi da laifin aikata rashawa.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: