Tuesday, 29 January 2019
Amfanin Zuma Ga Jikin Dan Adam

Home Amfanin Zuma Ga Jikin Dan Adam
Ku Tura A Social Media
Zuma dai wani ruwa ne mai zaki, wanda masana a fannin kiwon lafiya suka tantace kuma suka tabbatar da zakin shi bai da wata illa ga jiki ko rayuwar bil'adama. Hasalima Zuma na samar da kariya ga bil'adama a kan wasu cututtuka daban-daban. Cikin wasu alfanun Zuma ga jikin bil'adama, mun yi kokarin zakulo muku wasu kadan daga ciki wadanda suka hada da:
1🐝. Masana sun tabbatar da cewa Zuma na rage barazanar cutar sugar ko diabetes ga jikin bil'adama.
2🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na rage radadin cutar mura (respiratory infection or cough).
3🐝. Masana har ila yau sun tabbatar da cewa Zuma na rage barazanar cutar gyambon ciki (Ulcer).
4🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na taimaka wa bil'adama wajen buda masa huhu yadda zai yi numfashi ba tare da wahala ba.
5🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na rage radadin cutar asma wanda in aka yi dace yakan kawar da cutar gabadaya.
6🐝. Masana sun tabbatar da cewa Zuma na kawar da cutar daji (stroke).
7🐝. Masana sun kuma tabbatar da Zuma na taimaka wa jikin bil'adama wajen narkar da abinci (improve digestion).
8🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na kara karfin kashi (active borne).
9🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na warkar da rauni ko kunar wuta a jikin bil'adama.
10🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na samar da sinadarin glucose ga jikin bil'adama wanda hakan na kara wa garkuwar jikin kuzari (boost immune system).
11🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na gyara fatar jikin bil'adama (skin beauty).
12🐝. Masana sun kuma tabbatar da cewa Zuma na dauke da sinadarin amino acids wanda yana rage yawan nauyin jiki ko kiba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: