Kiwon Lafiya

Amfani Da Citta Fiye Da Kima Na Iya Sanadiyar Zubar Da Ciki

 By Idris Aliyu Daudawa Wani kwararra kuma masaniyar cututtukan da suka jibanci mata da kuma kananan yara wadda take aiki a ‘Life Line Children Hospital’ da ke Lekki, Lagos, Misis Aledis Essie.
ta ja hankalin mata masu juna biyu, akan shan ko kuma amfani da Citta mai yawa.
Essien ba bayyana hakan ne a wata ganawa da tayi da wakilinmu, ta ce Citta tana yin sanadiyar kamuwa da Kunar Zuci ga wadanda suke da cutar gyambon ciki da aka fi sani da ‘ulcer’.
Ta ci gaba da bayyana cewar, “ Duk da yake tana da muhimmanci ga lafiyar mata masu juna biyu, amma idan basu sha da yawa ba, amma idan aka sha da yawa, tana iya zama sanadiyar yin bari .
“ Duk da yake dai ba wai ance tana da hatsari bane, amma wannan sai an sha wadda bata kai 1500mg ba.
Amma kuma ya dace mace mai ciki ta tuntubi Likitan ta kafin ta sha, saboda zata shafi mizanin sikarin ta idan tana da Ciki.
Ga wadanda suke da cutar sikari, yana da kyau su tuntubi Likitansu, wannan kuma ya danganta ne, idan sun tuntubi Likitan sune cewar za su yi amfani da Citta lokacin Juna biyun su.”
Don haka ta ba mata masu Juna biyu shawarar da su guji amfani da ita, idan suna da tarihin, yadda suke zubar da jini ta mafitsarar su, shiga wani yanayi na jiri, ko kuma “clotting” da kuma yin bari.
Kamar dai yadda kafar sadarwa ta “parenting.firstcry.com,’ ta bayyana cewar amfani da Citta b wadda bata wuce misali ba lokacin da mace take dauke da Juna biyu ko kuma (Ciki) yin hakan yana taimakawa lura da mizanin ‘cholesterol’ da kuma bunkasa yadda jini ke zuwa ga abin da ke cikin mahaifa.
Idan mace mai Juna biyu tana amfani da Citta ana samun ci gaba wajen karuwar jinin dake zuwa wurin abin da ke mahaifa.
Citta tana da amfani wajen samar da waraka ko kuma sauki ga wadanda suke bda matsalar ciki, ko kuma yin Amai da safe wayanci wannan mata masu ciki suke fama da wannan..
Tana taimaka ma jiki ya samu wasu sinadarai daga abincin da aka ci.
Amfani da Citta kafin mai Juna biyu ta kwanta hakan yana taimaka mata wajen samun sauki daga matsalolin da ta kan fuskanta, misali matsalar da ake fuskanta daga cin abinci mai yawa, da kuma kayan sha masu yawa, ga kuma al’amarin daya shafi yinTusa ko kuma Kumburin ciki.
 Tana kuma taimakawa wajen samun saukin ciwon jiki da kuma samar da sinadaran Iron da kuma Bitamin amma kuma sai ana shan ta ba da yawa ba.
Tana kuma taimakwa wajen wajen bunkasa kwayoyin halitta na jariri.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?