Thursday, 3 January 2019
Ali Nuhu ya lashe kambun mafi kwarewa a bada umurni na 2018

Home Ali Nuhu ya lashe kambun mafi kwarewa a bada umurni na 2018
Ku Tura A Social Media
Shahararren dan wasan hausa na Kannywood da kuma Nollywood Ali Nuhu, ya lashe kambun gwarzon shekarar 2018 da ya fi kowa kwarewa wajen bayar da umurni
- Da aka fi saninsa da Sarkin Kannywood, Nuhu ya lashe kambun ne da fim din sa mai suna "Mariya"
- Fim din Mariya, ya ta'allaka ne akan auren wuri da ake yiwa mata a kasar Hausa
Shahararren dan wasan hausa na Kannywood da kuma Nollywood Ali Nuhu, ya lashe kambun gwarzon shekarar 2018 da ya fi kowa kwarewa wajen bayar da umurni, a bukin karramawar da Nothern Trendz ta shirya.
Da aka fi saninsa da Sarkin Kannywood, Nuhu ya lashe kambun ne da fim din sa mai suna "Mariya".
Nuhu ya walafa a shafinsa na Instagram @realalinuhu, "Karramawa ta farko a wannan shekarar, mafi kwarewa a bayar da umurni, da fim din Mariya"

Nuhu ya godewa wadanda suka shirya wannan karramawar, yayin da kuma a hannu daya ya goodewa wadanda suka taimaka har shirin fim din Mariya ya kammala.
Fim din Mariya, ya ta'allaka ne akan auren wuri da ake yiwa mata a kasar Hausa.
Daga cikin 'yan wasan da suka taka rawa a fim din akwai, Maryam Yahaya, wacce ta taka rawa a matsayin Mariya, sai Umar M. Shareef wanda ya taka rawa a matsayin Abdullahi, wanda shine masoyin Mariya na hakika, sai kuma Baba Karkuzu, dattijon da aka tilasta Mariya ta aureshi, inda ya tarwatsa mafarkinta na zama likita.
Ali Nuhu ne ya kasance wanda ya dauki shirin fim din, da bayar da umurni, tare da kasancewa daga cikin 'yan wasan shirin

Share this


Author: verified_user

0 Comments: