Tuesday, 22 January 2019
Ali Nuhu ya bayyana yanda wani tsohon jarumi ya rika shekar da kudinshi a wajan Caca

Home Ali Nuhu ya bayyana yanda wani tsohon jarumi ya rika shekar da kudinshi a wajan Caca
Ku Tura A Social Media


Ali Nuhu ya bayyana yanda wani tsohon jarumi ya rika shekar da kudinshi a wajan Caca
Tauraron fina-finan Hausa, Ali Nuhu, Sarki ya bayyana irin yanda wani tsohon tauraron fina-finan Hausa ya rika yin caca da kudin da yake samu daga masana'antar.

Alin ya bayar da martaninne a yayin da ake ciki da sukar taurarin fina-finan Hausa akan hirar da aka yi da Chiroki a tashar Arewa24 wanda ya nuna halin ni'yasu da yake ciki.
Wani ya rubutawa Alin cewa, Na ga karkuzu shima yana korafin irin wannan a wani lokaci da ya gabata cewa bashi da ko da daki daya na kanshi, mutumin ya kara da cewa wannan abin kunyane ga Kannywood.

Ali Nuhu ya bashi amsar cewa, A lokacin da yake caca da kudin da yake samu daga Kannywood ka bashi shawarar yayi abinda ya kamata? Dan Allah kar kasa mu fara tone-tone.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: