Labarai

Alherin Allah Ya Kai Ga Alhaji Atiku Abubakar kalla A Cikin Hotuna

Tsarki Ya tabbata ga Allah Maji rokon bayinShi, cikin kaddarawar Allah (SWT) sakon mu Ya isa ga cibiyar Atiku Care Foundation ta hannun mace mai kamar maza jaruma Hajiya Maimuna Yusuf, sunyi alkawarin daukar nauyin jinyar wannan bawan Allah Auwal Halliru Buharism

A yanzu haka wakilin Atiku Care Foundation zaije har gidansu Auwal Buharism ya dubashi, sannan zasu bashi naira dubu dari da hamsin (150,000) kyauta wanda za’ayi amfani dashi waken gabatar da dukkan gwaje-gwaje a asibitin koyarwa na Sir Abubakar Tafawa Balewa University Teaching Hospital Bauchi (ATUBU) da kuma gwajin da za’a masa a sabon asibitin Air Force Base dake hanyar zuwa Kano Bauchi, zuwa gobe Litinin insha Allah

Bayan gwaje-gwajen da za’a masa likitoci zasu fadi adadin kudin da za’a kashe wajen yin aikin gyaran lakarsa (spinal cord) da ta samu matsala tun a shekaran 2011 lokacin da ya fado daga kan bishiya wanda hakan ya haddasa bai iya tafiya, sannan jijiyoyin hannunsa suka samu matsala

Bayan tallafin naira dubu dari da hamsin da muka samu daga gurin Atiku, yanzu haka tallafin da jama’a suke bayarwa wannan bawan Allah Ya kai kusan naira dubu sittin da wani abu, jama’a da suka taimaka muna matukar godiya gareku Allah Ya biyaku da gidan Aljannah Madaukakiya

Wallahi ina cike da farin ciki marar adadi, tunda nake a rayuwata Atiku bai taba burgeni ba kamar a yau, babu abinda mutum musulmi zai aikata Allah Ya jikansa Ya tsundumashi a Aljannah fiye da taimakon marayu da gajiyayyu da majinyata irin wannan

Baba Atiku Abubakar mungode Allah Ya daukaka darajarka a duniya, a lahira Allah muke roko Ya tsundumaka a Aljannah don Rahamarsa Amin.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com
Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu, Editor in Chief at Hausaloaded.com

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
WeCreativez WhatsApp Support
Barka Da Zuwa Shafin HausaLoaded.Com Sunana "Abubakar" Wane Taimako Zan Iyayi? 👨‍🦱
👋 Hi, how can I help?