Sunday, 2 December 2018
Wata Sarauniyar Kyau Ta Kasar Rasha Ta Musulunta, Ta Kuma Auri Sarkin Malaysia

Home Wata Sarauniyar Kyau Ta Kasar Rasha Ta Musulunta, Ta Kuma Auri Sarkin Malaysia
Ku Tura A Social Media

 Watatsohuwar sarauniyar kyau ta kasar rasha da ta rike karagar shekaru uku da suka gabata ta musulunta. Tsohuwar sarauniyar mai suna Oksana Voevodina ta kuma zama sabuwar sarauniyar Malaysia bayan da ta auri sarkin kasar Muhammad V na Kelantan.

 Voevodina na da shekaru 25 a duniya yayin da sarkin ya ke 49, wato ya bata shekaru 24 kenan. Ita kuwa Voevodina na da shekara 22 a lokacin da ta lashe gasar sarauniyar kyau ta Rasha a 2015. An yi bikin Voevodina da sarkin ne a birnin Moscow a ranar 22 ga watan Nuwamba, kamar yadda jaridar New York Post ta rahoto. Voevodina dai ta zabi sunan Rihana a matsayin sabon sunanta na musulunci

Share this


Author: verified_user

0 Comments: