Monday, 31 December 2018
Wata Sabuwa: Adam A Zango Ya Mayar Da Martani Akan Masu Sukarsa Da Ya Kira Shugaban kasa Buhari Maulana

Home Wata Sabuwa: Adam A Zango Ya Mayar Da Martani Akan Masu Sukarsa Da Ya Kira Shugaban kasa Buhari Maulana
Ku Tura A Social Media


Tauraron fina-finan Hausa kuma mawaki, Adam A. Zango ya mayar da martani akan rubutunnan da yayi akan shugaban kasa, Muhammadu Buhari a shafinshi na sada zumunta da ya kirashi da Maulana kuma Muridin Allah daya jawo cece-kuce.


A cikin wani faifan bidiyon dai daya wallafa a shafinshi na sada zumunta, Adam yace, yayi rubutu akan Buhari inda ya kirashi da Maulana amma wasu suka wa kalmar mummunar fahimta, yace idan mutum bai san abinda ake nufi da abuba to yaje ya nemi sani, ya kamata masu sukar suje su nemi sanin kalmar dan a fassara musu. Yace shi bai yi laifi ba da ya fadi waccan kalma saboda Annabi(S. A. W) yace kada kawa abokin halitta biyayya musamman idan ya kasance yana sabawa Allahne.

Adamu ya kara da cewa da wannan na dogara nikewa Buhari addu'a da kuma wannan na dogara nikewa Buhari fatan Alheri da kuma wannan na dogara nike baiwa Buhari gudummuwa ta hanyar sana'ata.

Ya kara da cewa, kai kuma da kake saginshi ka sani cewa abinda kake fada zaka tashi gaban Allah ranar Qiyama ka maimaita dan haka ka fadi Alheri ko kai shiru.

Yaci gaba da cewa sannan wanda kake so ka tabbata ko wanene kamin ka soshi bawai kawai dan an baka kudi ba, ka kuma tambayi me zai maka me zaiwa 'ya'yanka da jikokinka da addininka da kuma al'adarka.

Yace sannan a cikin matasa irina ko sa'annin Buhari babu wanda zai ce maka Buhari barawone, ko Buhari fasikine ko Buhari Mushirikine ko Buhari azzalumine, yace dan haka kamar yanda wani shugaban mu ya bayyana da musulmi azzalumi gara wanda ba musulmi ba adali ballantana mu musulmine kuma Adali muka sa agaba kuma muke masa fatan Alheri.

Dan haka ni banga aibunshiba ko abinda zaisa in kushe shiba ko kuma ince ban yadda da mulkinshi ba, kaima haka sai kace ga abinda da abinda naka ke da shi, bazan zagi naka ba kaima karka zagi nawa, babu wanda zai ce maka dan me kake son naka koma waye, watakila ya fi Buhari kai a ganinka amma ni Buhari na gani kuma shina yi bincike akai na gamsu kuma ina fatan Allah ya bashi hudu sau hudu sau hudu ya maimaita.

@hutudole

Share this


Author: verified_user

0 Comments: