Tuesday, 11 December 2018
WASANNIZa Mu Yi Raga-raga Da Barcelona, Inji Kociyan Tottenham

Home WASANNIZa Mu Yi Raga-raga Da Barcelona, Inji Kociyan Tottenham
Ku Tura A Social Media
Kocin kungiyar kwallon kafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino, ya ja kunnen ‘yan wasan sa cewar Barcelona ba za ta yi musu sako-sako ba, idan suka hadu a gasar cin kofin Zakarun Turai a wasansu na yau. Tottenham ta samu karfin gwiwar zuwa Spaniya, bayan da ta doke kungiyar Leicester City da ci 2-0 a ranar Asabar a gasar firimiya a wasan mako na 16 wanda hakan ya karawa ‘yan wasan kungiyar karfi da gaske. 

Kungiyar ta Ingila ita ce ta biyu a rukuni na biyu a gasar ta Zakarun Turai da maki bakwai daidai da na Inter Milan, saboda haka da zarar ta ci Barcelona za ta kai wasan zagaye na biyu kenan. Ita kuwa Inter Milan wadda za ta kece raini da PSB mai maki daya kacal a ranar ta Talata, tana sa ran a doke Tottenham a Spaniya, ita kuma ta ci wasanta ta kai zagayen gaba a gasar. Pochetino ya ce za su fuskanci kalubale kuma duk da Barcelona ta kai zagaye na biyu, a gasar Zakarun Turai babu batun daga kafa kuma suma dole sai sun dage sun saka a ransu cewa zasu iya samun nasara akan Barcelona har gida. Pochettino yace kungiyar Barcelona ba karamar kungiya bace saboda haka dole sai ‘yan wasanmu sun dage domin ganin sun bawa duniya mamaki ta hanyar yiwa Barcelona raga-raga  a filin wasa na Nou Camp.   

©leadershipayau.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: