Saturday, 15 December 2018
Sholaye Jeremi ne uban ɗana – Fitacciyar marubuciya, Linda Ikeji, ta tabbatarwa duniya a wani rubutu mai ratsa zuciya

Home Sholaye Jeremi ne uban ɗana – Fitacciyar marubuciya, Linda Ikeji, ta tabbatarwa duniya a wani rubutu mai ratsa zuciya
Ku Tura A Social Media

Fitacciyar marubuciyar nan ta turanci, Linda Ikeji, mai shafin nan mai farin jini da ke kawo muku labarai da tsegumi da gulma da duminsa, ta fito ta warware tinja-tinjar da ke kewaye da yaron da ta haifa a kwanakin da suka gaba. Inda ta bayyanawa duniya waye uban dan nata.

Lindar ta yi wannan warwara ne a wani rubutu da ta fitar a yau, Juma’a 14 ga watan Disamba, 2018. Ga bayanin Linda:

Kawanaki biyu rak gabanin ranar zagayowar ranar haihuwa ta ta cika shekaru 38, wannan rana ta zo daidai da 17 ga watan Satumba ta shekarar nan da muke ciki na 2018 ne na haifi dana da na sanya wa suna Jayce. Na dubi shi (jaririn), wannan ya jefa ni cikin tunanin dalilin da ya sanya na bata lokaci haka ban haihu ba. Me ya sa na bari sai yanzu? Na tambayi kaina.

Ban taba jin ina kaunar wani abu a duniya ba yadda na ke jin so da kaunar abinda na tsuguna na haifa. Na kasa gaskata cewa daga jikina ya fito. Ko shakka babu dana shi ne kyautar da Ubangiji ya yi mini mafi daraja, kuma a shirye nake na bashi kulawa da tarbiyya iyakar iyawa ta..


In muka koma kan dalilin da ya sanya na yi wannan rubutu, sai na ce muku na dade ina shawarwari akan na bayyana ainahin labarina ko kuma na bari.. faga karshe dai na yanke hukuncin cewa, labarina labari da ya dace na rubuta kuma na watsa shi a duniya don makaranta su karanta musamman saboda ‘yan mata na kasa da ni da suke kallo na a matsayi wata abar koyi.

‘Yan matan da na yi tasiri wajen saisaita rayuwarsu, da wadanda nake kan yi wa rayuwarsu saiti da ma wadanda zan yi wa a nan gaba. ‘Yan matan da na ke baiwa horo akan yadda za su tafikar da rayuwarsu ta yadda za su cimma buri da mafarkinsu. Ta yadda za su san ‘yancinsu da kuma yadda za su kadin ‘yancin nasu in an tauye musu. Kwatsam kuma sai ga shi ni na je na haifi da gabanin na yi aure. Ko shakka babu wannan zai iya jefa wadanda suke kallo na a matsayin misali cikin halin rudu musamman ma yadda aka yi ta sakin labaran kanzon kurage daban-daban game da ni. wanda ya fi bani dariya shi ne wai wani mai aure ne ya yi min ciki har na haihu.

Ga amsa ta ga wadanda ke cewa mai aure ne ya yi min ciki…….

Za mu ci gaba da wannan wasika ta Linda gobe da yardar Allah
@alummata.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: