Sunday, 9 December 2018
Shirin ‘Gizo Da Basamude’ Na Kannywood Ya Doke Sauran Finafinai A Bajekoli Na Kasa

Home Shirin ‘Gizo Da Basamude’ Na Kannywood Ya Doke Sauran Finafinai A Bajekoli Na Kasa
Ku Tura A Social Media

 Wani fim din Hausa na tatsuniyar Gizo Da Basamude na wani matashin Kannywood mai suna Sulaiman Surajo, wanda a ka yi amfani da hoton zane (animation) wajen shirya shi ya zama gwarzon fim na shekara a Najeriya. Gizo da Basamude ya zama gwarzon shekarar ne a bikin bajekoli na Zuma Film Festibal da a ka gudanar a Abuja cikin makon da ya gabata, inda a ranar Juma’ar nan a ka rufe bajekolin da bikin mika kyaututtuka ga finafinan da su ka yi zarra a taron. Wannan ba karamin abin nasara ba ne ga masana’antar Kannywood, saboda yadda fim din ya gwabaza da finafinan Kudu da ma na wasu kasashe da su ka halarta, amma ya doke su, ya zama na daya. Hakan ya kuma nuna yadda masana’antar ke cigaba da bunkasa ta fuskar kwarewar aiki. Shi dai Sulaiman Surajo matashi ne dan asalin jihar Kano mai shirya finafinai a kan kwamfuta, kuma ya samu kwarewar aiki ne a Najeriya da kasar Ingila. A kwanakin baya ma fim din na Gizo da Basamude ya samu fitowa a jerin finafinan da su ka kai matakin karshe a gasar bikin bajekoli da a ka gudanar a kasar Kenya tare da wani fim din Hausa shi ma daga Kannywood mai suna Juyin Sarauta. Shi dai Juyin Sarauta shi ne ya zama gwarzon fim na harshen cikin gida a gasar ta bajekolin Zuma a bara.

©leadershipayau


Share this


Author: verified_user

0 Comments: