Labarai

Shawaran Datti Assalafiy zuwa Ga Mai girma shugaban kasa Muhammadu Buhari

Ina maka fatan alheri Maigirma shugaban ‘kasa Muhammadu Buhari.
Kasancewar mu anan Nigeria Allah Ya jarrabemu da wata babbar matsala ta yanda kafin mutun ya samu ikon ganin shugaban ‘kasa ko ya aike masa da sako sai yasha wahala, domin munga lokacin da Minista mai ci akayi yunkurin hanashi ganin shugaban ‘kasa balle sauran ayari gama garin talakawan Nigeria, don haka babu wata hanya da ta rage mana wajen isar da sako ga shugaban ‘kasa fiye da yin amfani da kafofinmu na sada zumunta da Allah Ya hore mana

Maigirma shugaban ‘kasa ni Datti Assalafiy na kasance daya daga cikin dunbin masoyanka wanda Allah Ya fahimtar dasu abinda ya shafi tattara bayanan sirri tsaro (Intelligence gathering) da hanyoyin magance barazanar tsaro da ayyukan ta’addanci (Peace and conflict resolution) kullun burina a rayuwa shine na samu zaman sirri da kai domin baka tawa gudunmawa wajen tabbatar da tsaro a ‘kasarmu Nigeria

Ina matukar adawa da dukkan abinda zai taba gwamnatinka ya nuna gazawarka Yaa Maigirma shugaban ‘kasa babban burina shine kaci nasara a shugabancinka, jiya talata naji wai ka jagoranci zaman tattaunawa da wasu masu ikon tsaro akan abinda yake faruwa a jihar Zamfara, da kuma matakin da ka dauka na tura shugaban sojojin saman Nigeria zuwa jihar Zamfara, wannan mataki da ka dauka zai taimaka

Amma bayan haka nazo maka da wata shawara wanda zai taimaka kwarai dagaske, duk da dai a tsorace nake saboda tsoron gujewa makircin maciya amana wanda basa kaunar a samu zaman lafiya a Nigeria, amma mawuyacin halin da ake ciki musamman a Zamfara yasa zan sake bada tawa gudunmawa na shawara kamar haka:
A shekarar 2004 tsohon shugaban Nigeria Olusegun Obasanjo ya kawo wani tsari a hukumar ‘yan sandan Nigeria na inganta tsaro daga ‘kasar Ingila, tsarin da a turance ake kira da (Community Policy) karkashin wannan ne nakeso na bada shawara

Maigirma shugaban ‘kasa, ka bada umarni wa rundinar sojin Nigeria ta nemo maka duk wani soja da ya fito daga jihohin Borno da Zamfara masu mukami daga Laftanar (Lieutenant) zuwa Kanar (Colonel), sannan kayi irin wannan umarni ga rundinar ‘yan sandan Nigeria ta nemo maka dukkan wani jami’in ‘dan sanda da ya fito daga jihohin Borno da Zamfara masu mukami daga Mataimakin sufurtendan ‘yan sanda (Assistant Superintendent of Police ASP) zuwa mukamin Kwamishinan ‘yan sanda Commissioner of Police CP)

Maigirma shugaban ‘kasa idan aka nemo maka adadin wadannan jami’ai, sai kabi file dinsu ka karanci irin record da kowanne daga cikin jami’an yayi breaking a aikinsa na tsaro, wadanda sukafi jarunta da kwazo da basira da ilmi akan tsaro da rashin tsoro daga cikinsu zai ka zabesu, su kai adadin kananun hukumomi dake jihohin Borno da Zamfara, sai kasa a kira maka su, ka nemi zaman tattaunawar sirri tsakaninka da su

Idan ka tattauna dasu sai kace zaka basu wani national assignment, wadanda suka fito daga Borno zaka turasu Borno, wadanda suka fito daga Zamfara zaka turasu Zamfara, don haka su fadi dukkan abinda suke bukata na kayan yaki da ababen hawa, kuma su fada maka adadin kudin alawus na kula da walwalarsu da na kananun jami’ai wanda zasuyi aiki karkashinsu da za’a bukata tun kafin a fara yakin, sannan ka basu damar da zasu karbi umarni kai tsaye daga gareka a filin yaki

Daga nan Maigirma shugaban ‘kasa sai kasa rundinar soji da na ‘yan sanda su nemo kananun jami’an tsaro wadanda suka fito daga jihohin Borno da Zamfara, sai kasa suyi aiki tare da wadancan manyan ofisoshi da ka zabo ka karanci record dinsu, kuma kowace karamar hukuma a tura jami’an tsaron da suka fito daga karamar hukumar tare da Kwamandansu ‘yan asalin karamar hukumar

Manufar hakan shine; jami’in tsaro da ya fito daga inda aka haifeshi zaifi kowa sanin sirrin yankinsa da harcen yaren kabila da akeyi a yankinsa, yana daya daga cikin abinda muka karanta a ilmin tsaro ba zaka iya cin nasaran tabbatar da tsaro a wani yanki ba matukar bakasan sirrin gurin ba, ba zaka dauko inyamuri daga jihar Abia sai ka turashi jihar Borno cikin kabilar Kanuri kace ya yaki Boko Haram har ya kai ga nasara ba, gaskiya haka bai taba faruwa ba a tarihin yakukuwan duniya

Maigirma shugaban ‘kasa idan ka dabbaka wannan shawaran sai ka basu lokaci kace kana son kafin lokacin ya kare ba’a sake yin garkuwa da wani mutum a jihar Zamfara ba, ‘yan ta’adda basu sake kawo hari a ko’ina a jihar Borno ba, ka tabbata alawus dinsu mai kauri yana shiga akan lokaci, jami’an tsaron zasuyi aiki tukuru domin sun san al’ummarsu ne, jama’arsu zasu kare kuma mahaifarsu

Ina fata Allah Ya sa wannan shawara tawa zata isa ga Maigirma shugaban ‘kasa ya kuma dubeta da idon basira Amin

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button