Sunday, 30 December 2018
NASARA DAGA ALLAH Boko Haram Ba Su Ji Da Dadi Ba A Hannun Sojoji A Yankin Baga Dake Jihar Borno

Home NASARA DAGA ALLAH Boko Haram Ba Su Ji Da Dadi Ba A Hannun Sojoji A Yankin Baga Dake Jihar Borno
Ku Tura A Social Media

Daga Datty Assalafiy

Kamar yadda mai magana da yawun rundinar sojin saman Nigeria Air Commodore Ibikunle Daramola ya tabbatar, yace Boko Haram din da suka kutsa yankin Baga da zummar kwace ikon garin abin bai musu dadi ba, sun hadu da mummunan ajalinsu sakamakon ruwan wuta da manyan jiragen yakin Nijeriya suka zuba musu.

Akwai sojojin ruwa a Doron Baga, lokacin da 'yan ta'addan sukayi yunkurin gudawa ta wannan bangaren sojojin ruwan sunyi amfani da manyan jiragen ruwa na yaki suka fatattakesu adadi mai yawa.

Yace har zuwa yanzu ba'a kai ga tantance adadin 'yan ta'adda da jiragen suka hallaka ba, yayin da sojojin 'kasa suka sake karban ikon garin na Baga.

Makiya zaman lafiyar Nijeriya da 'yan adawar gwamnatin shugaba Buhari ba su ji dadin wannan nasara da aka samu ba.

Allah Ka karawa dakarun mu nasara. Amin.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: