Tuesday, 11 December 2018
Najeriya Ta Lallasa Kasar Libya A Wasan Kwallon Yashi

Home Najeriya Ta Lallasa Kasar Libya A Wasan Kwallon Yashi
Ku Tura A Social Media
Tawagar kwallon kafa ta Najeriya Super Eagles mai wakiltarta a gasar kwallon yashi ta nahiyar Afrika, ko kwallon bakin teku dake gudana a kasar Masar, ta samu nasarar farko bayan soma gasar. Najeriya wadda ke rukunin B, ta lallasa kasar Libya da kwallaye 6-3 a wasan da suka fafata na ranar Lahadi wasan day a dauki ‘yan kallo sakamakon itama kasar Libyan ba kanwar lasa bace. 

A wasan farko dai Super Eagles din na kwallon kafar yashi, sun yi rashin nasara ne da kwallaye 2-0 a bugun daga kai sai mai tsaron gida, a hannun takwarorinsu na Senegal masu rike da kofin gasar, bayan tashi wasan farkon da suka fafata 4-4. Su kuwa Libya sun lallasa Tanzania da kwallaye 5-0 ne a wasan farkon da suka buga hakan yabawa kasar Libyan kwarin gwuiwar tunkarar wasan na Najeriya sai dai basuyi nasara ba kamar yadda suka tsara. A yau Talata Najeriya za ta fafata wasan karshe na cikin rukuni- rukuni da kasar Tanzania, wadda a jiya Litinin ta sha kashi a hannun kasar Senegal da kwallaye 12-2, wasan daya bawa duniya mamaki.

 Kasar da ta lashe kofin gasar kwallon yashin da kuma ta biyu ne za su wakilci nahiyar Afrika a gasar kwallon yashin ta duniya da kasar Paraguay za ta karbi bakunci a sabuwar shekara mai kamawa.     

©leadershipayau.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: