Monday, 24 December 2018
Matsayin Sanya Turare A Al'aurar Mace A Musulunci -Daga Sheikh Kabiru Gombe

Home Matsayin Sanya Turare A Al'aurar Mace A Musulunci -Daga Sheikh Kabiru Gombe
Ku Tura A Social Media


Fitaccen malamin addinin musuluncin nan a Najeriya Sheikh Kabiru Gombe, ya ce sanya turaren miski, wanda aka fi sani da Musk Dahara a al'aurar mace ba shi da wata illa, kuma sunna ce mai karfi.
Likitoci da dama dai sun sha yin kira ga mata da cewa su daina sanya duk wani sinadari walau turare ko sabulu ko ma dai mene ne a al'aurarsu, saboda hakan yana da illa matuka wajen kashe wasu kwayoyin halitta da ke zagaye da farjin nasu, wadanda aikinsu shi ne su kare wajen daga saurin kamuwa da cuta ko wacce iri ce.
A cewar su, bincike ya nuna cewa yawan amfani da duk wani abu mai sinadarai a al'aura, kan jawo yaduwar kwayoyin cuta a wajen, ta yadda idan abin ya yi tsanani ya kan jawo fitar wani ruwa mai launin dorawa ko kore, mai kuma wari.
"Wasu kuma ya kan sanya musu kuraje da kaikayi mai tsanani," kamar yadda wasu kwararrun likitocin mata Dr Hauwa Isa, da Dr Hauwa Shu'aibu, da kuma Dr Yalwa Usman suka shaida wa Halima Umar Saleh.
A hirarsa da BBC dai Sheikh Kabiru Gombe ya ce ko a musulunce ba ko wanne turare ake so mace ta sanya a al'aurarta ba don tabbas ba za a rasa masu cutarwa ba.
Ya ce turaren Musk Dahara, wanda shi ne ainihin wanda Nana Aisha RA ta yi amfani da shi, shi ne kadai ingantacce da ake so a yi amfani da shi.
Sheikh Gombe ya kara da cewa ko Musk Dahara din ma ba ko wanne lokaci za a sanya ba sai a lokacin da mace ta kammala al'adarta, saboda ya taimaka wajen kawar da karnin jini.
'Bincike na iya sauyawa'
Sheikh Kabiru Gombe ya kara da cewa duk da cewa likitocin sun ce bincike ne ya nuna haka, 'su ko yaushe a cikin bincike suke, kuma binciken nasu ya kan sauya daga lokaci zuwa lokaci, ba mamaki gobe kuma su gano wani abun da zai sauya wannan matsaya ta su.
"Ita kuwa maganar addini wahayi ne daga Ubangiji zuwa wajen Manzonsa SAW wadda ba ta sauyawa," a cewar Sheikh Gombe

Share this


Author: verified_user

0 Comments: