Saturday, 29 December 2018
Maganar Gaskiya Ni ban taba Yin wa'azi Akan wai Ado Gwanja ya warware mana wa'azin Da muke Aka mata Ba- Sheikh Dr. Kabiru Gombe

Home Maganar Gaskiya Ni ban taba Yin wa'azi Akan wai Ado Gwanja ya warware mana wa'azin Da muke Aka mata Ba- Sheikh Dr. Kabiru Gombe
Ku Tura A Social Media

✍️ Ibrahim Baba Suleiman

Shararren Malamin Addinin Musulunci Sheikh Dr. Muhammad Kabir Haruna Gombe, ya kalubalanci masu yada jita jita a kafafen sadarwa ta zamani da su kawo masa muryar inda yace ya dau shekara da shekaru suna yiwa mata wa'azi, amma Dare daya Wani mawakin hausa wai shi Ado Gwanja ya warware wa'azin. Wai a cewar su tunda Ado gwanja yace mata suyi sama, tunda sukayi sama har yanzu basu dawo ba. Kabir Gombe yaci gaba da cewa a ina yayi wannan wa'azin? A kawo masa Murya yaji in da gaske yayi wa'azin zai bada tukwici ga Wanda ya kawo masa murya.

Shehin Malamin yace yana mamakin mutanen da suke zama su tsara labarin da babu shi, kawai Dan su yada karya cikin mutane.

Haka zalika wani makiyin Allah ya bude Account na Twitter da "Sheikh Kabiru Gombe" yana ta rubuce rubucen da bai kamata ba, kawai dan ya damfari mutane da sunansa, babu gaira babu dalili, duk kuwa da ansa kwararrun jami'an tsaro da masana su binciko shi, kuma zasu binciko mai aiki da wannan account insha Allah.

A karshe Dr. Kabir Gombe, yayi addu'an Allah ya shiryi masu irin wannan hali, in kuma ba masu shiryuwa Bane Allah ya mana maganin su.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: