Sunday, 9 December 2018
Hukumar NYSC ta soke bautar kasar Davido,

Home Hukumar NYSC ta soke bautar kasar Davido,
Ku Tura A Social Media

Hukumar NYSC ta soke bautar kasar Davido, sai ya sake tun daga farko duk kuwa da yamadidi da akayi tayi a kasar nan, kan bautar kasar masoyin waka David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, yanzu dai mawakin yace hukumar NYSC ta soke bautar kasar tasa, a shafinsa na Instagram.

A cewarsa dai, dama yazo ne yayi bautar kasar saboda ya sami damar toshe duk wata kafa da nan gaba ka iya kawo masa illa, ganin yadda 'yar takardar ta NYSC ta kori minista sukutum daga aiki a kasar nan.

Matashin wanda shekarunsa 25, ya kammala karatunsa na digiri, fannin kida a jami'ar Babcock, a 2015,amma sai yanzu ne ya gwammace yayi bautar kasar don kar ya zama ya kai 30 bai yi ba.

A yayin da yake taya abokinsa murnar gama tasa bautar kasar ne, wanda ya saka takardarsa a shafin Instagram, Adesegun Adeosun, yana neman a taya shi murna, sai Davido yace: "Na so dem cancel my own oo." Inda yake nufi"a haka ni kuma suka soke min nawa fah!"Dama dai idan mutum ya fiye fashi a aikin NYSC, to za'a soke aikin nasa na shekara, kuma dole ya dawo badi ya sake aikin a rabin albashi, wato N9,900. A maimakon N19,800 da ake biyan kowanne kopa a wata.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: