Friday, 7 December 2018
Ganduje Ya Nemi Mawakan Kannywood Su Yi Wa Buhari Sabbin Wakoki

Home Ganduje Ya Nemi Mawakan Kannywood Su Yi Wa Buhari Sabbin Wakoki
Ku Tura A Social MediaGwamna Ganduje ya bukaci masu shirya finafinai Hausa da mawakansu da cewa su tabbatar da fitar da sabuwar waka da sabon fim don takarar shugaban kasa Muhammad Buhari musamman kan nasarorin gwamnatin cikin shekaru uku da rabin da suka gabata, haka kuma su fito da sabbin dabarun samun Karin nasarar takarar ta shugaban kasa da kuma Jam’iyyar APC a zabe mai zuwa. Gwamna Ganduje ya kuma jinjinawa kyakkyawar gudunmawar da suke bayarwa a harkokin siyasa musamman ganin yadda lokacin zabe ke kara gabatowa, ya ce siyasa ba tare da mawaka da sauran masu shirya finafinai ba la mi ce, saboda haka ya wajaba ku fahimci cikakkiyar rawar da ta kamata ku taka aduk wani yanayi na tsare tsaren yadda za’a tabbatar da samun nasarar zabe. Gwamna Ganduje na wannan jawabi ne a rana litinin data gabata alokacin da masu shirya finafainai da mawakan suka ziyarce shi a fadar gwamnatin Kano, taron da aka tsara domin saduwa da juna domin kara dakon zumunta na cikin wani bangare na tsare tsaren yakin neman zaben tare da kaddamar da yakin neman zaben Gwmna Gnaduje. Yace yana daga cikin abubuwan da suka kamata ku dauka domin ciyar da jam’iyyarmu ta APC da sauran masu neman takarkaru a mukamai daban daban tun daga kan shugaban kasa har zuwa kan majalisar dokokin Jihohi. Yace gudunmawarku na da muhimmancin gaske a tarihi kasar nan tun kafin samun ‘yancin kai, a cewar Gwamna Ganduje. Don haka Sai Gwamna Ganduje ya fito da wasu bangarorin da ake bukatar tabawa a lokutan gabatar da wakoki da finafainai, yace dukkan ku kuna sane da cewa kafin shekara ta 2015 yana wahalar gaske samun irin wannan dama sakamkon matsalar tsaro da wata irin barazana musamman kan abubuwan dake faruwa alokacin matsalar tsaro. A cewar Gwamna Ganduje, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu nasarar tabbatar da tsaro a fadin kasar nan, domin sai da ta kai an kawar da masu tada kayar baya daga wasu sassan kasaar nan, ba kamar yadda suka mamaye wasu yankuna ba lokacin da suke kan bakarsu. Gwamna Ganduje ya alkawarta shirya wani taro wanda za’a gabatar da wakokin siyasa tare da sauran masu gudanar da wannan harkoki, a lokacin bikin za’a yiwa wadanda suka taka muhimmiyar rawa wasu kyautuka inda zaku baje kolin basirar da Allah ya baku domin gamsar da al’umma. Lokacin bikin ana sa ran dukkan sakatarorin Jam’iyyar APC na kananan Hukumomin JIhar Kano 44 zasu halarci bikin kamar yadda Gwamnan ya ambata wanda zasu tafi da faya fayen wakokin da aka wallafa domin isar da su lungu da sawon Jihar Kano. Hakazalika Gwamna Ganduje ya karfafawa mawakan da kuma masu shirya finafinan guiwa da cewar za’a samar da tallafi gare su tare da basu shaidar samun horo da zasu shiga alokaci mai zuwa, yace da wannan takarda shaida zaku samun damar amfana da damammaki masu yawa, babu shakka wannan takardar shaidar zata taimaka kwarai da gaske wajen ciyar da wannan tsari da kuma bangaren da kuka fi kwarrwa akansa. Haka kuma Gwamnan ya yi alkawarin ci gaba da binciko hanyoyin tallafin daga gwamnatin tarayya ta yadda zasu ci gaba samun rance daga bankin dake lura masana’antu Da suke gabatar da nasu jawaban daban daban guda cikin shugabannin masana’antar shirya finafinai, Alhaji Baba Karami bayan daukar dogon lokacin yana zayyana ire iren nasarorin wannan Gwamnati, ya alkawartawa Gwamna Ganduje yin duk mai yiwuwa domin fitar da sabbin wakoki wadda zasu karade lungu da sakon wannan kasa domin neman nasarar wannan Gwamnati, sannan kuma ya bukaci ci gaba da tabbatar da kyakkyawar dangantakar da ke takanin gwamnati da masu gudanar da wannan sana’a. Cikin wadanda suka tofa albarkacin bakinsu alokacin taron akwai Dauda Kahutu Rarara, Nura Husaini, Jamila Nagudu, Alasan Kwalle, Tijjani Asase, Shehu Hassan Kano,Naziru S. Ahmad, Dauda Kahutu Rarara, Fati Niger, Jadda Garko, Ibrahim Ibrahim, Yammedi, Ado Gwanja da sauransu. Haka kuma shugaban kungiyar mawakan Kwankwasiyya Tijjani Gandu ya bayyana dalilan kowamarsa Jam’iyyar ta APC inda yace yanzu ya yiwa gwamnatin Ganduje kyakkyawar fahimta ne tare da tabbatar da samun nasarar Gwamna Ganduje alokacin zabe mai zuwa. Kamar yadda mai Magana da yawun gwamnatin Kano Abba Anwar ya shaidawa Jaridar LEADERSHIP A Yau Juma’a. 

Share this


Author: verified_user

0 Comments: