Wednesday, 26 December 2018
Duk Wanda Ya Kashe Wani A Kaduna Sai Na Sa Hannu An Kashe Shi - El-Rufa'i

Home Duk Wanda Ya Kashe Wani A Kaduna Sai Na Sa Hannu An Kashe Shi - El-Rufa'i
Ku Tura A Social Media

A wata tattaunawa ta musamman da muka yi da Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa'i ya bayyana cewa, duk wanda ya kara yin kisa a jihar Kaduna da gangan, shima sai ya sa hannu an kashe shi.

Gwamnan ya bayyana haka ne yayin amsa tambayar matakin da ya dauka domin dakile rikicin kabilanci da ya faru a jihar.

"A baya idan aka yi rikici a jihar Kaduna ba a daukar matakin hukunta masu laifin. Amma yanzu mun kama su mun kai su kotu an tura su kurkuku. Sannan wasu sun gudu muna kuma bin diddigin wayoyinsu. Kuma duk wanda ya kashe wani haka kawai idan kotu ta yanke masa hukuncin kisa sai na sa hannu an kashe shi. Domin shima wani ya kashe".

Share this


Author: verified_user

0 Comments: