Wednesday, 5 December 2018
Dan sarkin Kano, Aminu Sanusi Zai Angonce; kalli zafafan Hotunansa Da Amaryar Da zai Aura

Home Dan sarkin Kano, Aminu Sanusi Zai Angonce; kalli zafafan Hotunansa Da Amaryar Da zai Aura
Ku Tura A Social Media


Dan mai martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Aminu Sanusi, na shirin angincewa yayinda ya watsa zafafan hotunan kansa da amaryar da zai aura a sashen Instagram.

Yayinda ya daura hotunan a yammacin jiya, Aminu ya siffanta a matsayin zinariyarsa.

Yace: “Babu wani abu da suna mata mara aibi ko aure mara aibi…Abinda kawai ya kamata mu bukata shine mata mai fahimta da karamta miji. Daga karshe, na samu zinariyata saboda haka, ina gabatar muku da sabuwar gimbiyar Kano, Fulani Zainab Ali Bashir.”


Share this


Author: verified_user

0 Comments: