Saturday, 1 December 2018
Daga karshe Dai Obasanjo Ya Shiga Ya Fita Amarka Ta Baiwa Atiku Bizar Shiga Kasar Ta

Home Daga karshe Dai Obasanjo Ya Shiga Ya Fita Amarka Ta Baiwa Atiku Bizar Shiga Kasar Ta
Ku Tura A Social Media

Daga karshe dai Kasar Amurka ta baiwa dan takarar Shugabancin kasa a karkashin inuwar Jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar damar shiga kasar ta.

Hakan ya biyo bayan cece-kuce a tsakanin Ya'yan Jam'iyyar APC da kuma Ya'yan Jam'iyyar PDP kan batun baiwa Alhaji Atiku Abubakar damar shiga kasar ta Amurka gabanin zabukan 2019 dake tafe.

A makon daya gabata ne Ministan yada labaru Lai Mohammed, ya gargadi kasar Amurka kan kada ta sake ta baiwa Atiku Abubakar damar shiga kasar ta.

Dama dai an zargi Alhaji Atiku Abubakar da hannu cikin haumahaumar cin hanci da rashawa wanda wani rahoto ya bayyana cewar an hana Atiku shiga kasar.

Yanzu haka dai wani rahoto ya bayyana cewar an dankawa Atiku Abubakar Bizar damar shiga kasar kuma tsohon shugaban kasa Olushegun  Obasanjo, ya taka rawar gani wajen ganin Atiku ya karbi Bizar.

Daga yanzu zuwa ko wane lokaci Atiku Abubakar zai iya bayyana kasar Amurka, wani rahoton da wani na kusa da Atikun ya bayyanawa manema labaru yace Atiku zai fita zuwa kasar London daga bisani kuma zai ketara zuwa Amurka.

Daga :Jaridar Dimokuradiyya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: