Saturday, 29 December 2018
Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai

Home Da duminsa: Rundunar 'yan sanda ta fara farautar Dino Melaye akan yunkurin kisan kai
Ku Tura A Social Media

Rundunar 'yan sanda ta ce akwai wasu tambayoyi da take son Sanata Dino Melaye ya amsa a gabanta kan zargin da take masa na yunkurin kisan kai

 - Rundunar 'yan Sanda ta yi zargin cewa Melaye da tawagar 'yan ta'addansa sun harbi wani Sajen Dajuma Saliu a jihar Kogi, a ranar 19 ga watan Yulin 2018 - 

Rundunar ta ce jami'anta zasu ci gaba da zaman jira a gaban gidan dan majalisar dattijan, har sai sun tabbata sun cafke Melaye Rundunar 'yan sanda ta ce akwai wasu tambayoyi da take son Sanata Dino Melaye ya amsa a gabanta kan zargin da take masa na yunkurin kisan kai Rundunar 'yan Sanda ta yi zargin cewa Melaye da tawagar 'yan ta'addansa sun harbi wani Sajen Dajuma Saliu tare da raunata shi, wanda ke kan aikinsa akan titin Aiyetoro Gbede zuwa Mopa a jihar Kogi, a ranar 19 ga watan Yulin 2018. Kakakin rundunar, DSP Moshood Jimoh, ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai, biyo bayan wata mamaya da jami'an rundunar suka kai gidan Melaye da ke birnin tarayya Abuja a ranar Juma'a. 

A cewarsa, masu bincike na rundunar 'yan sanda sun aikewa majalisar dattijai wasika, inda suka bukaci Melaye ya gurfana a ofishin rundunar na jihar Kogi, Lokoja, don amsa wasu tambayoyi kan zarginsa da ake yi, wanda kuma yaki amsa wannan gayyatar. Jimoh ya ce: "Melaye da tawagar 'yan ta'addansa ne suka aikata laifin a jihar Kogi a ranar 19 ga watan Yulin 2018, inda suka harbi Saliu da ji masa ciwo. Har yanzu jami'in na kwance yana jinyar wannan rauni da ya samu daga harin sanatan." Rundunar ta ce jami'anta zasu ci gaba da zaman jira a gaban gidan dan majalisar dattijan, har sai sun tabbata sun cafke Melaye.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: