Saturday, 22 December 2018
Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Magidanta Masu Mata Daidai Da Samari Masu Shirin Yin Aure

Home Budaddiyar Wasika Zuwa Ga Magidanta Masu Mata Daidai Da Samari Masu Shirin Yin Aure
Ku Tura A Social Media

Assalamu alaikum `yan uwa magidanta da masu niyyar zama.

Zan so in dan kawo muku wannan dan tsokaci nawa, domin me yiwuwa ya haska wa wadansunku hanya a yayin da Allah ya sake hada su da wata da suke son su shigo da ita cikin gidansu, domin ta zama daya daga cikin gungun iyalinsu, ko ma uwar `ya`yansu.
Mata sai kana karatu akan dabi`unsu da kuma fahimatar halayensu wadanda na halitta ne da Allah yayi musu, da kuma wadanda son zuciya ne da son kai ya sa suka kirkiro wa kansu. Idan har ka fahimci haka, duk lokacin da daya daga ciki ya faru, sai ka yi kokarin maganinsa ko toshe shi, ba tare da shedan ya samu kafar da zai kutso ya lalata zaman lafiya da kwaciyar hankalin gidanka ba.

Me neman karin aure ina so ka fahimci mata ta wadannan bayanai da zan zaiyano maka kamar haka :-

1. Duk wata `ya mace tana da kishi, sai dai wajen baiyana shi ne da daukar mataki aka banbanta.
2. Duk namijin da yayi wa matarsa abokiyar zama to a wajenta ya yi mata laifi, ko da kuwa rayuwar sahabban Manzo (saw) yake shimfida musu a gidan nasu.
3. Duk matan da suka fi daya a wajen maigidansu, to ko wacce so take ta karbe fada a wajen maigidan nasu, ko da kuwa nagartarta ta kai ta matan sahabban Manzo (saw).

4. Duk namijin da yake auren mata fiye da daya, to yana cikin tarkon zargin yin rashin adalci mara yankewa, ko da kuwa kwanciya yake ko wacce dayarsu ta zauna akan gadon bayansa.
 Idan har ka fahimci mata akan wadannan batutuwa na sama, ka sani cewa:

A duk lokacinda ka yi nufin karin aure, sai ka yi taka tsantsan domin kada ka fada kogin nadama, kayi shirin tinkarar kalubalen da ke fuskantar ka gida da waje, ta gida tana ganin ka butulu, an ci amfanin ganga an ya da kwaure, ta waje tana nuna maka cewa da zarar ka aure ta, matsalolinka na rayuwar aure sun kare.
Hmm, maigida a dai yi hattara, ta gida ka san halinta, ta san naka, ka zama ita, ta zama kai, ta waje kuwa lalube kake cikin duhu, ba za ka taba sanin cikinta da banta ba sai ta shigo gidanka, ba kuma za ka gane hakikaninta ba sai ka hau dokin zuciya ka kori wacce ta tarar a gidanka.

Nasihata gare ku ita ce: ko da ta gida dukanka take ka kyale ta da halinta, domin idan ka sake ta, me yiwuwa wacce ta shigo yankan naman jikinka za ta rika yi.
Babban makaminka shine; ka shimfida adalci a gidanka, ka zama alkali ba lauya ba, ka zama aboki ba mai mulkin kama karya ba, ka zama me nasiha ba me fada da banbami ba, abinda hakuri bai kawo shi ba, rashin hakuri ba zai samar da shi ba.

Da zarar ka yi nufin karin aure, ka rubanya kyautatawar da kake yiwa ta gida, ka zauna da ita ka lallabe ta, ka gamsar da ita ta yadda za ta hakurkurtar da zuciyarta, domin gamsarwa ta yadda da ingancin yunkurinka  ba me sauki ba ne. Ka toshe kunnanka game da furucinta da yake nuna bacin ranta ko kuma damuwarta, ka rufe idanunka game da abubuwanda da za ta yi maka domin gamsar da kai cewa ka yi bankwana da zaman lafiya a gidanka.

Ka sani cewa duk barazana, da tayar da hankali, da fadar bakaken maganganu, da gori za su yi sanyi daga baya, matukar ba ka ba wa shedan damar ya rinjaye ka a tsakankanin wadannan kwanaki har ka tanka mata, ko ka tsinke igiyar aurenku ba.

Maza da mata Allah ya ba mu juriyar hakuri da juna. Ba wani bangare da zai rayu ba tare da daya bangaren ba.
IDAN KUNNE YA JI .....
Bissalam naku

Share this


Author: verified_user

0 Comments: