Sunday, 16 December 2018
Barayi sun fasa motar General BMB sun sace mai makudan kudi

Home Barayi sun fasa motar General BMB sun sace mai makudan kudi
Ku Tura A Social Media
Tauraron fina-finan Hausa, Bello Muhammad Bello, General BMB ya bayyana cewa ya tashi da safe ya tarar wasu sun fasa mai mota sun dauke wasu kayayyaki da makudan kudi.A wani faifan bidiyo da ya saka a dandalinshi na sada zumunta, Bello ya nuna motar tashi da fasassun gilasai sannan ya bayyana cewa, wanda suka yi wannan danyen aikin sun sace mai kudi miliyan daya da kusan dubu dari uku.

Ya kara da cewa, koma meye Allah na nan kuma insha Allahu a karo na gaba zaku yi a bakin ranku.

Allah shi ya bani kuma zai sake bani In Sha Allah.

Muna fatan Allah ya kiyaye na gaba ya kuma mayar da Alheri.
Sources hutudole

Share this


Author: verified_user

0 Comments: