Wednesday, 12 December 2018
Ban Cika Abota Da Mata Ba Mafi Yawan Abokai Na Dukkan Su Maza Ne - Nafisa Abdullahi

Home Ban Cika Abota Da Mata Ba Mafi Yawan Abokai Na Dukkan Su Maza Ne - Nafisa Abdullahi
Ku Tura A Social Media


Daya daga cikin manyan Mata daga cikin Jaruman masana'antar shirya Fina finan Hausa Kannywood, Nafisa Abdullahi tace ita bata cika yin abota da Mata ba mafi yawan abokan ta Maza ne har cikin masana'antar su.

Jaruma Nafisa wacce aka fi sani da "Sai wata rana"tace bata cika shiga shirgin Jarumai mata na masana'antar Kannywood ba hasalima Halima Atete ce kawai suke yin waya da kuma wasu mu'amalolin na yau da kullum, amma ita tafi harka da mazajen masana'antar amma kuma ba wai suna fada bane aa kawai yanayinta ne haka.

Tun daren jiya Talata a wata hira ta musamman da jarumar tayi a lokacin data amsa gayyatar kafar yada labaru ta BBC Hausa Jarumar ta bayyana haka.

Jaridar Dimokuradiyya ta ruwaito cewar, Nafisa tace ita daga ciki jaruman Hausa fim tana shiri da dukkan su harma ta bayyana sunayen wasu daga cikin Jaruman kamar su Sadic Sani Sadic da Zaharaddeen Sani da kuma Abdul M Shareef, sai dai tace Ali Nuhu ba abokinta bane ya wuce gaban aboki a gurinta ta bashi matsayi na musamman.

A lokacin da jarumar take amsa tambaya game da Adam A Zango, tace eh sun yi soyayyah da Jarumin amma yanzu basa tare kusan shekaru hudu amma har yanzu suna girmama juna.

Share this


Author: verified_user

1 comment: