Tuesday, 4 December 2018
Babu wanda ya isa ya Hana : Fim Manyan Arewa Sun Fi Kishin Fina-Finan Kudu A Kan Na Arewa - inji Falalu Daurayi

Home › › Babu wanda ya isa ya Hana : Fim Manyan Arewa Sun Fi Kishin Fina-Finan Kudu A Kan Na Arewa - inji Falalu Daurayi

Post By:

Ku Tura A Social Media

Bayan Manyan Arewa sun ki amsa gayyatar sabon shirin da kanwar tsohon Shugaban kasa Murtala Ramat, mai suna Baraba Ramat ta dauki nauyi" Daraktan shirin Falalu Daurayi ya fusata"

Darakta kuma jarumi Falalu Daurayi ya yayyarfa bakaken maganganu game da rashin halartar manya kasar nan wajen bikin kaddamar da sabon shirin.

Baraba Ramat ta dauki nauyin wani sabon shiri a Kannywood mai suna JUYIN SARAUTA wanda shirin ya sami Lambar girma 8 kuma har yanzu babu kamar shi a masana'antar Kannywood, abun mamaki wajen kaddamar da shirin Manyan Arewa sun ki zuwa idan anyi magana kuma sai suce mu yan Kannywood bama koyi da Al'adar Arewa to idan ita baza su amsa gayyata saboda ita ba suyi mata kara saboda Dan'uwanta mana Margayi; inji Falalu

Falalu ya bayyanawa wakilin mu Shuaibu Abdullahi haka ne rashin a bace da yammacin yau Litini bayan bullar wannan bidiyon da zamu wallafa muku labarin dashi,yace sau uku yana halartar biki kaddamar da shiri na mutanen kudu su ana kyautata musu amma Yan Fina finan Arewa bata su ake yi ba.

Sabon shiri mai take JUYIN SARAUTA wanda yanzu haka babu kamar shi a Kannywood Falalu ne Daraktan shirin kuma Ado Ahmad Gidan Dabino ne mashiryin shirin kuma an yi biki kaddamar dashi a Meena Event dake Jihar Kano, wanda Hajiya Balaraba Ramat Muhammad ta dauki nauyi.


 Ku saurari bayyaninsa da kunnuwanku daga babban daraktan kannywood.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: