Sunday, 23 December 2018




Baba Buhari A Jingine Kamfen Ana Shan Jinin Talakawa A Zamfara

Home Baba Buhari A Jingine Kamfen Ana Shan Jinin Talakawa A Zamfara
Ku Tura A Social Media

Daga Rabiu Biyora

Yanzun nan na amsa kiran waya daga wani Babban mutum dan jihar Zamfara inda yake bayyana mun irin tashin hankalin da mutane suka shiga a garin Maradun da Dan Magaji da suke jihar Zamfara, ya sanar dani cewa jiya wasu Makasa sun kashe mutane masu yawa a wadannan garuruwan ciki harda sirikinsa, yayi mamakin yadda Makasan suka dauki dogon lokaci suna gudanar da ta'adanci....

"Wallahi Biyora kashe kashen nan dake faruwa suna rage darajar Muhammadu Buhari a idanun talakawan Zamfara, har mamaki suke yadda Gwamnatin ke fuskantar matsalarsu duk da irin tarin kaunar da suke masa, ka tambayi abokanka dake jihar Zamfara zasu gaya maka sabon sunan da wasu suka sakawa Shugaba Buhari duk akan wannan matsalar dake faruwa, babban abun damuwar shine yadda mutane suke neman juyawa APC baya a jihar suna furta cewa baa damu da rayuwarsu ba baa dagewa wajen kokarin kawo karshen kashe kashen da akeyi musu.....

Don Allah Rabiu Biyora kuyi amfani da Social Media ku sanar da wannan lamari dake faruwa a jihar Zamfara, wallahi muna kaunar Baba Buhari ko kadan bamajin dadin yadda yake rasa masoya da kima a idanun talakawan Zamfara, duk da cewa ya bawa dan jihar Zamfara mukamin ministan Tsaro, amma gaskiyar magana abun dake faruwa yana janyo matsaloli masu yawa yanzu haka.....

HOTON DANA SAKA TSOHO NE....

Nayi amfani dashi don isar da sako kamar yadda aka nemi inyi....

Allah Ya bamu zaman lafiya

Share this


Author: verified_user

0 Comments: