Monday, 10 December 2018
BA ZA MU ZABI BUHARI BA - Dattawan Arewa

Home BA ZA MU ZABI BUHARI BA - Dattawan Arewa
Ku Tura A Social Media


Kungiyar dattawan arewacin Najeriya da ake kira Northern Elders Forum ta sanar da janye goyon bayanta ga sake zaben shugaba Muhammadu Buhari.

Shugaban kungiyar Farfesa Ango Abdullahi ya shaida wa BBC cewa sun yanke wannan shawarar ne saboda abin da ya kira "ba wani abin ci gaba da Buhari ya yi wa arewa a kusan shekaru hudu na mulkinsa."

"Buhari ya gaza wajen magance talauci da matsalar ilimi a arewacn Najeriya," in ji Farfesa Ango.

Ya ce arewacin Najeriya ne dandalin talauci, kuma yankin ne ya dage wajen ganin Buhari ya lashe zaben shugaban kasa a 2015.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: