Tuesday, 11 December 2018
Ba Laifi Ba Ne Yin Jima'i A Cikin Mota – Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya

Home Ba Laifi Ba Ne Yin Jima'i A Cikin Mota – Rundunar 'Yan Sandan Nijeriya
Ku Tura A Social Media

Daga Wakilinmu Yaseer Kallah

Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta ce mutum bai aikata laifi ba idan ya aikata jima'i a cikin motarsa.

Sai dai rundunar 'yan sandan ta ce zai iya zamowa laifi matukar mutum ya yi jima'in da karamar yarinya, ko kuma idan ya faka motar a wani gurin bauta a sa'ilin da yake jima'in.

Bayan nan rundunar 'yan sandan ta kara da fadin laifi jima'in cikin mota idan mutane biyun jinsinsu daya.

Saboda haka, rundunar 'yan sandan ta fitar da sanarwar cewa dukkan wani wanda aka nemi ci masa mutunci domin ya yi jima'i a cikin mota ya gaggauta kai mata rahoto.

Shugaban sashin karban korafe-korafen al'umma na rundunar ta 'yan sandan Nijeriya, Mr. Abayomi Shogunle ne ya bayyana hakan yayin da yake bayar da amsar wata tanbaya da aka masa ta shafinsa na Twitter.

An ta yin tanbayoyi a shafukan sada zumunta game da wannan batun bayan da wasu tarin mutane suka ci mutuncin wasu ma'aurata bayan sun gan su suna jima'i a cikin mota.

Da ya ke amsa tanbayar, Shogunle cewa ya yi, "A'a. Jima'i a cikin mota a guraren mutane ba laifi ba ne a Nijeriya matukar gurin da suke yi ba gurin ibada ba ne; mutane biyun 'yan shekara 18 ne zuwa sama; akwai amincewar juna (ba fyade ba ne); mutane biyun ba jinsinsu daya ba.

"Idan an yi barazanar kama ka a kan hakan ka kai rahoto ga 'yan sanda."

Share this


Author: verified_user

0 Comments: