Sunday, 16 December 2018
An Fara Nuna Fim Din Hausawa Na Turanci A Sinimar Kano

Home An Fara Nuna Fim Din Hausawa Na Turanci A Sinimar Kano
Ku Tura A Social Media
Bayan tsawon lokaci da aka shafe ana aikin kasaitaccen fim din nan na Turanci wato In Search of the King, wanda Malam Kabiru Musa Jammaje ya dauki nauyin shiryawa, a yanzu haka dai fim din ya kammalu har ma an fara nuna shi a sinima da ke cikin babban kantin sayayya na Shoprite dake kan titin gidan namun daji a Kano. An fara nuna fim din ne a shekaranjiya Jumaa 14 ga watan Disamba, da misalin karshe 5 na yamma, wanda kuma dumbin masu sha’awar kallon fim din suka shiga domin kallon sa. Za a iya cewa dai fim din ya kasnace wani zakaran gwajin dafi a finafinan da ake nuna wa a sinimar cikin watanin nan, domin kuwa daga yadda dumbin masu kallo suka cika sinimar hakan ya zo da bazata, domin kuwa an duaki lokac mai tsawo ba a samu fim cin d aya samu jama’a masu yawa a wjaen kallon sa ba. Shi dai fim din In Search of the King labarin wani matashi ne mai suna Bello (Abdullahi Amdaz) wanda ya kasance mai faftukar neman ilimi da kuma son ya ilmantar da jam’a, wanda a dalilin haka ne ya yi tafiya mai nisan zango tare da shiga cikin masarautu domin yada ilimi kuma ya sha fama da gwagwarmaya kafin ya cimma nasarar zuma sarki mai daraja ta daya.


 A fim din an fito da martabar ilimi da kuma matsayin jagoranci, sannan uwa uba an yada ilimin addini da jagoranci, yayin da iya ma al’adar kasar Hausa ta zamo ado a cikin fim din. Don kuwa an nuna zahirin yadda gidan sarautar kasar Hausa yake da kuma adda sarakuna suke tafiyar da sarautarsu. Ta bangaren zalunci da kuma tausayawa ga talakawansu. Wani daga cikin wadanda suka kalli fim din a rana ta farko da muka ji ta bainsa bayan fitowarsa daga kallon cim din ya shaida mana cewar, “A gaskiya ban yi asarar lokacina ba domin kuwa fim din ya gamsar da ni sbaoda yana fita da sakon da yake dauke da shi kuma abin alfahari ne a gare mu mu Hausawa a ce mun yi fim irin wannan da turanci don ni dai ban taba ganin fim din d aya fito da al’adar mu kamar fim din In Search of the King ba,  ga dai ba da Hausa aka yi shi ba amma labarin duk na kasar Hausa ne, kuma abin da ya kara burge ni da ya kasance Hausawa ne suka yi shi, don in da kamar wasu ne suka zo suka yi ai ka ga za su saka ra’ayinsu a ciki wanda kuma hakan zai kai ga gurbata wata al;adar tamu ta kasar Hausa. Ita ma wata daliba mai suna Ruwayya Abdullahi wadda take karatu a jami’ar Bayero ta bayyana mana cewar, “Ni na zo kallon fim din ne da na ji an ce na turanci ne kuma yana ba da tarihin kasar Hausa, don haka na zo, don na ga irin turancin da aka yi amfani da shi. to gaskiya abin ya birge ni don a matsayi na na daliba na karu da wasu kalmomin turanci da aka yi amfani da su don haka ina jinjina wa malam Kabiru Jammaje da wannan kokari da ya yi. Za dai a shafe tsawon mako biyu ana nuna fin din a sinimar wato daga nan zuwa karshen wata. Kuma fim ne da fitattun jarumai na masana’antar finafina ta Kannywood irin su Ali Nuhu, Baballe Hayatu, Abba Almustapha, Nafisa Abdullahi, Asma’u Nas, Rabi’u Rikawada, Shehu Hassan Kano, Rukayya Dawayya, Mustapha Musty, Yakubu Muhammad, Saratu Gidado, Shu’aibu Yawale suka jagoranci fim din.   

Share this


Author: verified_user

0 Comments: