Monday, 24 December 2018
Alherin Allah Ya kai Ga Dattijo Mai Tausayin Talakawa Alhaji Atiku Abubakar

Home Alherin Allah Ya kai Ga Dattijo Mai Tausayin Talakawa Alhaji Atiku Abubakar
Ku Tura A Social Media


Jama'a idan zaku tuna kwanaki 3 da suka gabata mun fitar da sanarwa na wata yarinyar marainiya 'yar shekara 13 da haihuwa, sunanta Aisha Haruna da take tare da mahaifiyarta a unguwar Rahamawa dake garin Daura jihar Katsina wacce ta hadu da tsautsayi na kunar wuta wanda ya mata illa sosai, mukace aje a bincika a tabbatar don a tallafa mata

AlhamdulilLah bayan sanarwan ya yadu Baba Atiku Abubakar yaga sanarwan ya tura wakilcin kungiyarshi na "Atiku Care Health Foundation" sun dauki nauyin jinyar yarinyar, daga karshe sun dauketa daga garin Daura suka kaita asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano  (Aminu Kano Teaching Hospital)

A halin yanzu har an mata aiki kuma tana  samun lafiya sosai..
Mutanen mu da muke tsammani zasu taimaka wa rayuwar yarinya sun kasa yin komai kansu kawai suka sani, sai 'yan adawarmu a siyasa ne sukayi

Baba Atiku mungode kwarai dagaske bisa ceto rayuwar marainiyar Allah da kayi
Kaima muna maka fatan Allah Ya ceceka ranar Hisabi, Allah Ya biya maka dukkan bukatunka na alheri Amin.

Daga:Datti assalafiy

Share this


Author: verified_user

0 Comments: