Wednesday, 19 December 2018
Abinda Pogba yayi bayan da aka kori Mourinho da ya dauki hankulan Duniya

Home Abinda Pogba yayi bayan da aka kori Mourinho da ya dauki hankulan Duniya
Ku Tura A Social Media

Bayan da labarin korar me horas da kungiyar Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana, masu sharhi da dama sun ta tunanin ganin ko me Pogba zai ce akan hakan.


Ai kuwa sai gashi Pogban ya saka wani hoto inda yake murmushi me alamar tambaya a dandalinshi na sada zumunta sannan ya tambayi mabiyanshi cewa me zaku ce akan wannan?

Da yawa sun caccaki Pogban bisa nuna rashin sanin ya kamata da yarinta da kuma wasa da sana'arshi akan wannan hoto dake nuna alamar cewa kamar yaji dadin korar da akawa Mourinhon.

Dama dai sun dade suna samun sabani tsakaninsu.

Aikuwa irin daukar hankalin da hoton yayi nan da nan ba'a dade ba sai Pogban ya cireshi daga shafin nashi amma tuni ya riga ya watsu.

Saidai wani rahoto daga shafin AS na cewa, wanan fa ba lallai bane akan korar da akawa Mourinhone Pogban ya saka wannan hoto ba, tana iya yuwa kuma akwai alamun kasancewar kamfanin Adidas ne Pogban yake wa talla, wadda aka yi ta akan gaba.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: