Tuesday, 6 November 2018
Zamu Kifar Da Gwamnatin Najeriya Matukar Ba A Saki Zakzaky Ba - 'Yan Shi'an Iran

Home Zamu Kifar Da Gwamnatin Najeriya Matukar Ba A Saki Zakzaky Ba - 'Yan Shi'an Iran
Ku Tura A Social Media

Wani bidiyo da aka sanya a yanar gizo ya nuna wasu ‘yan shi’a ‘yan kasar Iran suna barazanar tumbuke Buhari daga kan mulki idan har ba a saki Sheik Ibrahim El-Zakzaky ba.

Tun a watan Disambar 2015 ne El-zakzaky ke rike a hannun jam’an tsaro bayan wani rikici da ya kaure tsakanin ‘yan shi’an da sojojin Nijeriya.

‘Yan kungiyar sun sha gudanar da zanga zanga domin kira ga gwamnati da ta saki shugaban na su, amma gwamnatin ta yi kunnen uwar shegu, duk da cewa kotu ta bada umarnin yin hakan.

A bidiyon wanda jaridar The Cable ta wallafa, wasu masu zanga zanga ne ke waken “A saki Zakzaky” a turance.

Wani mutum wanda ya yi kama da shugaban tawagar ya soki gwamnatin tarayya a bisa ci gaba da rike El-Zakzaky da ta ke yi.

“Gwamnatin Nijeriya ta sani cewa ba za ta iya rike Zakzaky ba a har abada, In Sha Allah idan muka tumbuke gwmantin zalunci, za mu saki Zakzaky mu koya wa Nijeriya da mutanenta darasi mai kyau.”, Inji shi.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: