Monday, 19 November 2018
Zamfara Ta Dawo Danya: An Yi Garkuwa Da Mutum 45 A Shinkafi

Home Zamfara Ta Dawo Danya: An Yi Garkuwa Da Mutum 45 A Shinkafi
Ku Tura A Social MediaBayanai na nuna cewa, an sace mutum 45, ciki har da mata da kananan yara a karamar hukumar Shinkafi, wannna sace sacen sun faru ne a tsakanin ranar Alhamis zuwa ranar Asabar. Lamari na farko ya faru ne da safiyar ranar Alhamis a kan hanyar garin Kware zuwa garin Shinkafi inda aka yi awon gaba da mota dake dauke da mutum 35 a kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a garin na Shinkafi, inda aka kwashe dukkansu zuwa cikin daji na nufin yin garkuwa da su.

 Bayanan da suka fito daga wani day a bukaci a sakaya sunansa, ya nuna cewa, dukan muytane 35 sun fada hannun masu garkuwar ne a lokacin da suke kokarin fito da motarsu bayan da ra makale a cikin yashi. Daga nan ne suka ga ‘yan ta’addan sun fito su da yawa a kan mashina dauke da muggan makamai, inda suka zagaye mutane suka kuma yi awon gaba da su.

 An kuma ruwaito cewa, haka kuma a ranar Asabar, a yi sace mutum 11 ciki har da mace daya a kuyen Kware duk dai a cikin karamar hukumar Shinkafi, bayanai sun kuma nuna cewa an kashe mutum daya a lokacin da aka kawo harin. Jamiin watsa labarai na rundunar ‘yan sanda na jihar SP Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwa lamarin, ya ce, tuni a kan tura wata kakkarfar runduna ‘yan sanda don shawo kan wanna lamarin a karamar hukumar Shinkafi. Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu dukkan bangarorin jami’an tsaron jihar ciki har da sojoji sun shirya gudanar da ayyukan fatattakar ‘yan ta’adda daga dukan maboyarsu. 

SP Mohammed ya kuma kara da cewa, ‘yan sanda za su yi dukkan abin day a kamata na ganin an cafke ‘yan ta’addan gaba daya tare da kuma hukunta su.   

@leadershipayau.com

Share this


Author: verified_user

0 Comments: