Friday, 30 November 2018
Zaben 2019: Buhari Ya Shirya Magudi, Saboda Haka Za'a Fafata Sosai, Kafin Kawar Da APC – Atiku

Home Zaben 2019: Buhari Ya Shirya Magudi, Saboda Haka Za'a Fafata Sosai, Kafin Kawar Da APC – Atiku
Ku Tura A Social Media


Dan takarar shugaban kasa a Inuwar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya yi kira da a tsige Sufeto Janar din ‘yan sandan Kasa kafin zabukan 2019.

Atiku ya bayyana haka ne a wajen taron gaddamar da kwamitin kamfen din sa wanda shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki zai shugabanta.

Atiku ya ce dole wannan kwamiti su tabbata an tsige Sufeto Janr Idris kafin zabe domin babu alamar zai yi adalci a aikin sa.

” Dole ne mu tabbata an tsige sufeto janar din ‘yan sandan kasa kafin zabukan 2019. Wannan yana daga cikin manyan abubuwan da zamu sa a gaba.

” Bayan haka jam’iyyar APC ta koma sai tsikarar mu take gaba-gadi saboda gazawa da tayi na kawo sauyi na gari a kasar nan tun bayan hawanta karagar mulki a 2015.

” Za mu tunkari jam’iyya ce wato APC da take so ta ci gaba da mulki ko ta halin kaka. Wannan gwabzawa da za a yi a 2019 zai fi dukkan zabukkan da aka yi tun 1999.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: