Saturday, 17 November 2018
Yariman Saudiyya ne ya bayar da umurnin kisan Khashoggi

Home Yariman Saudiyya ne ya bayar da umurnin kisan Khashoggi
Ku Tura A Social MediaRahotanni daga Amurka sun ce hukumar leken asiri ta CIA ta yi imanin cewa Yarima mai jiran gado Mohammed bin Salman ne ya bayar da umurnin kisan dan jarida Jamal Khashoggi.
Wasu majiyoyi da kafofin yada labaran kasar suka ambato sun ce tuni hukumar ta sanar da bangarorin gwamnatin Amurka da suka hada da Majalisa kan binciken da ta gudanar wanda ya ci karo da ikirarin gwamnatin Saudiyya cewa ba hannun Yariman a kisan dan jaridar.

Wannan na zuwa bayan yin sallar Jana'izar marigayin a masallacin Ka'aba a Makka da na Madina a Saudiyya da kuma wasu masallatai a Turkiya da Paris da London.
Jaridar Washington Post da ta fara buga labarin ta ce binciken hukumar leken asirin Amurka ya gano cewa jami'an Saudiyya 15 sun yi amfani da jirgin gwamnatin kasar zuwa Santabul inda suka kashe Khashoggi a karamin ofishin jekadancinta da ke birnin.

Jaridar ta jiyo daga majiyoyi a hukumar na cewa tuni CIA ta sanar da gwamnatin Amurka da majalisa game da abin da ta gano wanda ya ci karo da ikirarin cewa Yarima bin Salman ba ya da hannu a kisan dan jaridar da ya fice wajen sukar manufofinsa.

Jaridar kuma ta ce Yarima Khalid bin Salman ne ya kira Khashoggi ta wayar tarho ya bukaci ya tafi Turkiya. Zargin da ya musanta a shafinsa na Twitter.
Gwamnatin Saudiyya ma ta fitar da sanarwa tana karyata rahoton binciken inda mai Magana da yawun ofishin jekadancin kasar a Washington ta ce wannan labari ne da ba ya da tushe.

Wannan na zuwa a yayin aka ruwaito cewa shugaban Turkiya Tayyip Erdogan da takwaransa na Amurka Donald Trump a wata zantawa da suka yi ta wayar tarho sun amince su yi aiki tare wajen dakile duk wani yunkuri na boye gaskiya game da abin da ya shafi kisan Jamal Kashoggi.

A ranar 2 ga watan Oktoba ne aka kashe Khashoggi a afishin jekadancin Saudiya da ke Santabul na Turkiya,
Kuma tuni Saudiya ta ce tana tsare da wasu da take zargi da kitsa kisan, yayin da tace wasunsu za su fuskanci hukuncin kisa.
Turkiya ta ce ba za ta amince da binciken na Saudiyya ba.
Mai bai wa shugaban Turkiya shawara, Yasin Aktay, ya ce "bincike ne da Yarima mai jiran gado ke jagoranta, bayan an ce ba ya da alaka da al'amarin."
"Ba za a taba tunanin samun adalci ba a kotun, dole Yariman ya kauracewa binciken idan gaskiya ake son ta fito," in ji shi.
A ranar Alhamis ne ministan harakokin wajen Saudiyya Adel al Jubair ya ce wasu ne da ba a san da su ba suka kashe dan jaridar.
Kuma ya ce ba hannun Yarima mai jiran gado a kisan.
A ranar Juma'a ne aka yi wa Jamal Khashoggi sallar jana'iza a masallacin Ka'aba a Makka da Madina da wasu manyan biranen duniya.
Kuma babban dan sa Salah Khashoggi ke jagorantar zaman makokin na kwanaki hudu tare da Iyalai da 'yan uwa da abokan arziki a birnin Jedda bayan ya koma daga Amurka.
An yi wa Khashoggi sallar jana'isa ba tare da gawarsa ba da har yanzu ba a san inda take ba inda wasu ke tunanin an boye ta ko kuma an narkar da ita ta hanyar amfani da sinadarin acid.
Turkiya ta ce tana da wani sakon murya na biyo da ta samu wanda zai dada cin karo da ikirarin da gwamnatin Saduiya ke yi cewa ba hannun shugabanninta a kisan Khashoggi.

Binciken CIA kuma a yanzu zai dada cin karo da kokarin Trump na kare amintakar da ke tsakanin Amurka da Saudiyya.

@bbchausa

Share this


Author: verified_user

0 Comments: