Tuesday, 27 November 2018
Wata cibiyar koyar da Bankin Musulunci ta rattaba Hannu da JIBWIS akan tallafawa gajiyayyu da nakasassu

Home Wata cibiyar koyar da Bankin Musulunci ta rattaba Hannu da JIBWIS akan tallafawa gajiyayyu da nakasassu
Ku Tura A Social Media

...Ta kuma yi yunkurin hada karfi da karfe da JIBWIS domin Assasa bakin musulunci

✍️ Ibrahim Baba Suleiman

Wata cibiyar koyar da bankin Musulunci mai suna 'Alhuda Center of Islamic Banking and Economics' ta shirya taro a kasar Dubai (United Arab Emirates) akan yakar talauchi a duniyar musulmi ta hanyar bankunan musulunci da wasu cibiyoyi masu yakar talauci da tallafawa ta tsarin shariar musulunci.

Cibiyar Al Huda cibiya ce wadda kasashen musulmi suka Amince dasu wajen koyar da tsarin bankin musulunci a fadin duniya.

Babban Bankin Jai'z dake Naijeriya ya samu halarta. Kazalika A taron an gayyaci kungiyar wa'azi ta musulunci dake Naijeriya, Izalatul Bid'ah wa iqamatis Sunnah (JIBWIS) saboda lura da akayi tana kokari wajen tallafawa nakasassu da hannu da kafafuwan roba kyauta wanda aka fi sani da shirin (M-sick),tare da tallafawa marayu a duk fadin kasa karkashin kungiyar IZALA.

Kazalika Bankin ya kara jinjina ga JIBWIS Akan kokarin magana da wayar da kan mutane Akan Sana'a, noma, da'awa da ilmantarwa. Kungiyar IZALA ita kadai ce kungiyar da aka gayyato a nahiyar Afurka ta yamma baki days, (West Africa) cikin kungiyoyin addini kuma aka karrama ta da Award na Best (Islamic organization on humanitarian services).

Taron ya samu hallartan kasashen Saudi Arabia, Pakistan, Indonesia, Malesia, China, Turkey, Kosovo, Azarbajan, Nigeria, Senegal, Morocco, Egypt, Kuwait, Sudan, Ethiopia, da sauransu.

A taron, kungiyar JIBWIS ta rattaba hannu na yarjejeniya (M.O.U) da wani bankin 'Micro finance' na musulunci daga pakistan Mai suna AKHUWAT kan taimakawa wajen Ilmi, Noma, Kiwon lafiya, da yakar Talauci tsakanin yan uwa musulmi.

Cibiyar takan shirya taron Kowa ce shekara, sannan kasashen musulmai Mafi yawa suna halarta, kuma Akan kai taron kasa kasa a bara anyi a turkey, shekara mai zuwa kuwa Azarbajan za'ayi insha Allah.

Wannan yarjejeniyar  zai koyawa JIBWIS dabarun noma, kiwo da yakar Talauci ta hanyar 'Micro Finance Bank'

Hoto: Yadda aka rattaba hannu  M.O.U tsakanin JIBWIS da bankin kamar yadda kuke gani.

Share this


Author: verified_user

0 Comments: